NCAA ta sammaci kamfanin jiragen Kenya kan wulanƙanta fasinjojin Nijeriya a Nairobi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta gayyaci kamfanin jiragen saman Kenya kan wani faifan bidiyo da ke nuna zazzafar husuma tsakanin wata fasinja ’yar Nijeriya da ma’aikatan jirgin Kenya a ofishin jigilar fasinjoji da ke birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

Wannan lamari ya biyo bayan wulaƙancin da kamfanin ya yi wa fasinjar, wanda ya zargi matafiyar ’yar Nijeriya da nuna rashin girmama wa ga ma’aikatansa ta hanyar jefar su da audugar mata.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani faifan bidiyo na riciki da aka yi tsakanin ma’aikaciyar kamfanin jirgin Kenya Airways da wata fasinja ‘yar Nijeriya, Gloria Omisore da ta tashi daga Legas zuwa Nairobi da Paris da Manchester ta jirgin ya bazu.

A cikin faifan bidiyon, ana iya ganin Omisore ta koka kan cin mutuncin da kamfanin jirgin ya yi mata, inda ta koka da yadda ba a kula da ita yadda ya kamata ba duk da cewa ta shafe sa’o’i 17 tana zaune.

Duk da haka, an ga ma’aikacin jirgin Kenya Airways tana gaya wa Omisore: “Ba za ki sake shiga jirginmu ba. Wannan wane irin hali ne? Kira shugaban ku. Ba za mu ba ki komai ba.”

Da yake mayar da martani ga faifan bidiyo a kan shafin Tuwita, Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Kayayyakin Kasuwanci a NCAA, Michael Achimugu, ya ce: “Babu wani uzuri na wulaƙanta fasinjar. Ma’aikatan jirgin ba su da ƙwarewa.

“Dole ne kamfanin jirgin ya ɗauki alhakin abin da ya faru da wannan fasinjar. Hukumar NCAA ta mayar da Kenya Airways zuwa kashi na 19 na dokokin NCAA na shekarar 2023, kuma ta gayyaci kamfanin zuwa hedikwatarta da ke Abuja a ranar Litinin 3 ga Fabrairu, 2025. Hukumar ta himmatu wajen kare haƙƙin masu ruwa da tsaki.”

A halin da ake ciki, da yake ƙarin haske kan lamarin, kamfanin jirgin a cikin wata sanarwa ya ce: “Baƙuwar ta za yi tafiya ne daga Legas zuwa Paris da Manchester. Lokacin da ta isa Nairobi don haɗewa saura fasinjoji zuwa Paris, an gano cewa ba ta da Biza ta SCHENGEN, wanda ke nufin ta shiga kowace ƙasa ta Tarayyar Turai. An ba ta madadin tafiya ta London zuwa Manchester, amma ta ƙi.