Hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta amince da buƙatar kamfanonin sadarwa na ƙara farashin sabis ɗin su wanda ya shafi kuɗin kira. Mai magana da yawun hukumar, Reuben Mouka, ya bayyana cewa an bayar da wannan amincewa ne bisa tanadin Sashe na 108 na dokar sadarwa ta Nijeriya, 2003 (NCA), wanda ya ba hukumar ikon tsara da amincewa da farashin sabis na kamfanonin sadarwa.
Mouka ya ce kamfanonin sadarwa sun nemi ƙarin farashin ne saboda yanayin kasuwar da ake ciki. Hukumar ta amince da ƙara farashin da ba zai wuce kaso 50 cikin 100 ba na farashin da ake amfani da shi yanzu, duk da cewa wasu kamfanonin sadarwa sun nemi ƙari sama da kaso 100. An cimma wannan matsaya ne tare da la’akari da gyare-gyaren masana’antar da za su kawo ci gaba da ɗorewa.
Hukumar NCC ta bayyana cewa sabon farashin zai kasance cikin tsarin da aka ƙayyade a nazarin farashi na 2013. Har ila yau, an tsara farashin daidai da jagorar da hukumar ta fitar a shekarar 2024 kan sauƙaƙa tsarin farashi. Mouka ya ƙara da cewa ƙarin farashin zai ba kamfanonin damar ci gaba da saka hannun jari a cikin kayayyakin aiki da sabbin dabaru, wanda hakan zai amfani masu amfani da sabis ta hanyar inganta sadarwa da ingancin cibiyoyin sadarwa.
A cewar NCC, an yi la’akari da halin da jama’a ke ciki wajen yanke wannan shawara, tare da tabbatar da cewa an cimma daidaito tsakanin kare masu amfani da sabis da kuma dorewar masana’antar. Haka zalika, an umurci kamfanonin sadarwa su tabbatar da yin bayani da bayyana sabbin farashin ga jama’a cikin gaskiya tare da nuna alfanun da sabis ɗin ya kawo. Wannan mataki, a cewar Mouka, zai tallafa wa bunƙasar tattalin arziƙin dijital na Najeriya.