Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Hana Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya, NCDC, ta bayyana fargaba a game da ɓullar sabuwar cutar korona a ƙasar Australia da ma wasu ƙasashe 42.
Yayin da ta ke bayani a kan sabuwar cutar ga jami’anta, ta buƙaci dukkan asbitoci na gwamnati da ma masu zaman kansu da su ƙara yin gwajin da suke a kan dukkan marassa lafiyar suke zargin sun kamu da sabuwar cutar Korona.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, NCDC, ta ce duk wani samfurin da aka samu yana ɗauke da cutar to a kai shi ɗakin gwaje gwajenta ko kuma wuraren gwajin da aka tantance.
Hukumar ta ce ta shirya tsaf domin tunkarar wannan matsala ta ɓullar sabuwar cutar Korona.
NCDC, ta ce yanzu haka sabuwar cutar ta ɓulla ƙasashen kamar Amurka da Indiya da Australia da Birtaniya da China da New Zealand da Thailand da Canada da Singapore da kuma Nijeriya.