NDLEA ta ƙwace kilo 251 na miyagun ƙwayoyi a Jihar Nasarawa

• Ta cafke masu fataucin ƙwayoyi 240 cikin wata shida

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Hukuma Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya (NDLEA), reshen Jihar Nasarawa ta ce ta ƙwace kimanin kilogiram 251 na miyagun ƙwayoyi a jihar.

Kwamandan hukumar a jihar, Peter Onche-Odaudu ne ya sanar da haka a jawabinsa a lokacin da yake ganawa ta musamman da manema labarai a shalkwatar hukumar dake birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar ranar Alhamis 23 ga watan Yunin shekarar 2022 da ake ciki.

Ya ce hukumar ta kuma cafke masu fataucin ƙwayoyin sama da 240 daga watan Janairu zuwa Yunin 2022 da ake ciki.

Kuma waɗanda aka kaman sun ƙunshi maza 235 da mata 5, a cewar shi.

Kwamandan ya qara da cewa kawo yanzu hukumar ta kuma gabatar da mutum 37 daga cikin waɗanda ta kamo a gaban kotu inda ake cigaba da shari’a akansu.

Ya cigaba da bayyana cewa, “ba shakka ɗaya cikin muhimman nasarori da muka kuma samu kawo yanzu shine na kamo wani babban mai fataucin hodar ibilis da aka fi sani da cocaine a wani otal da ke birnin Lafiya, inda muka kuma ƙwace cocaine ɗin.

“Kuma kamar yadda kuka sani wannan shine karon farko a tarihin jihar nan inda aka samu nasarar kamo mai harkar cocaine.”

Ya ƙara da cewa har ila yau sashen kula da masu taɓin hankali sakamakon shan miyagun ƙwayoyi na hukumar a cikin watanni 6 kacal ta warkar da mutum 3 daga cikin masu lalurar tavin hankalin waɗanda a yanzu sun samu cikakkiyar lafiya suna kuma gudanar da rayuwarsu cikin ƙoshin lafiya.

Sai dai duk da haka kwamandan hukumar a jihar, Peter Oduadu ya buqaci masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar baki ɗaya su haxa hannu su kuma cigaba da bai wa hukumar goyon baya a yaƙi da sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyin da take yi a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *