NDYC ta gargaɗi matasan Neja-Delta kan tashin hankali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Matasan yankin Neja Delta (NDYC) a ranar Talata ta buƙaci matasan da su guji ayyukan da za su iya lalata zaman lafiya da ake samu a yankin.

Shugaban hukumar na ƙasa, Abido Jator ne ya yi wannan kiran a Abuja, yayin da yake roƙon matasan da ke ƙoƙarin kada hankali da su janye zanga-zangar da suke shirin yi na nuna adawa da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).

Matasan sun zargi hukumar ta NDDC da cewa ba su ɗauke su tare da kuma kasa biyan buƙatunsu.

Jator ya ce, ƙungiyarsa ta daƙile zanga-zangar da matasan suka shirya a Unity Fountain da ke Abuja, inda ya ƙara da cewa, al’ummar yankin Neja-Delta sun yi tashe-tashen hankula kuma yanzu suna buƙatar su koyi zaman lafiya.

A cewarsa, zaman lafiya wani ɓangare ne na ci gaban zamantakewa da tattalin arziki ba makawa.

“A matsayinmu na ’yan ƙasa masu bin doka da oda da kuma mutanen Neja Delta, mun ga isassun tashin hankali, kuma muna buƙatar mu koyi jan hanyar zaman lafiya a yanzu.

“Yin ayyukan da za su iya lalata zaman lafiya mai rauni a halin yanzu a yankin Neja Delta da kuma Nijeriya, kuskure ne da bai kamata a yi la’akari da shi ba,” in ji Jator.

Shugaba ƙungiyar ya yi wa matasan alƙawarin zai yi amfani da matsayinsa wajen sa baki a lamarin domin magance rashin fahimtar juna cikin gaggawa.

Jator ya ce, su kama shi, idan hukumar ta kasa magance kokensu da biyan buƙatunsu.

“Ina da kwarin gwiwa ga gudanarwar yanzu da kuma Hukumar NDDC.

“Ina mai tabbatar muku da cewa ni da kaina zan gabatar da ƙorafinku, kuma a cikin kwarin gwiwa zan iya cewa ku riƙe ni, idan ba a magance kukan ku da wuri ba.

“Saboda haka, ku natsu kuma ku bi doka saboda komai zai yi kyau nan ba da daɗewa ba.

“Kamar yadda kuka sani, hukumar ta NDDC ta yanzu ‘yar kwakwalwa ce ta tayar da hankalin ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin farar hula don haka ba za su iya gaza mana ba,” in ji shi.