NED ta Amurka tana aikata mugunta da sunan dimokraɗiyyar ƙarya!

Daga CMG HAUSA

Kwanan nan ne, shugaban gidauniyar tallafin demokraɗiyya (NED), Dimon Wilson, ya jagoranci wata tawaga da ta kai ziyara yankin Taiwan na ƙasar Sin, inda ya fito ƙarara ya bayyana cewa, shi ne ya haifar da “juyin juya hali” a duniya.

Wannan muguwar ƙungiya ta yi tattaki zuwa ƙofar ƙasar Sin, don yin aiki da sunan demokuraɗiyya, a wani yunƙuri na haddasa “juyin juya hali”. Yadda take furta kalamai da ayyukanta, zai sa ta ci mummunan tura!

Kowa ya san wace ce gidauniyar tallafin demokraɗiyya ta ƙasa. Tun bayan kafuwar wannan ƙungiya mai zaman kanta da gwamnatin Amurka ke ɗaukar nauyinta, da nufin tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran ƙasashe da kuma gurgunta halastattun gwamnatocin wasu ƙasashe.

Mai fassarawa: Ibrahim