Neja: Gwamna Bello ya karɓi fasinjoji 39 da aka kuɓutar da su

Daga FATUHU MUSTAPH

Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya karɓi mutum 53 da aka yi garkuwa da su kwanan baya a motar sufuri mallakar gwamnatin Neja (NSTA).

Gwamnan ya karɓe su ne a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, babban birnin jihar bayan da aka samu nasarar kuɓutar da su daga hannun ‘yan bindigar da suka kwashe su.

Bello ya bayyana cewa, an yi nasarar kuɓutar da mutanen ne biyo bayan tattaunawa da dama da aka yi da kuma ƙwazon da gwamnati ta nuna.

Yana mai cewa an kammala dukkan shirye-shirye don binciken lafiyar mutanen kafin a sada su da iyalansu.

A cewar Bello, “Mun shafe mako guda muna tattaunawa da tuntuɓa, aiki tukuru da hana idanunmu barci domin ganin mun kuɓutar da su cikin taƙaitaccen lokaci.

“Mun kammala dukkan tsare-tsare domin binciken lafiyar mutanen, bayan kammalawa za mu miƙa su ga iyalansu.”

Gwamna Bello ya nuna godiyarsa ga Allah Maɗaukaki wanda Ya sahale musu ikon kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwar da su. Haka nan, ya yi godiya ga ɗaukacin waɗanda suka bada gudunmuwa wajen kubutar da wadanda lamarin ya shafa.

Mutum 53 da lamarin ya shafa 20 daga cikinsu mata ne, maza 24 sannan ƙananan yara su 9.

Idan dai za a iya tunawa, Manhaja ta ruwaito labarin sace fasinjojin mako guda da ya gabata, wanda ya auku a ƙauyen Kundu cikin ƙaramar hukumar Rijau ta jihar.

Game da ɗaliban Sakandaren Kagara da malamansu da aka yi garkuwa da su kwanan nan, Belli ya ce har yanzu suna hannun ‘yan bindigar, amma cewa gwamnati na ci gaba da yin abin da ya kamata don ganin su ma an kuɓutar da su lami lafiya.