Neja: An yi garkuwa da mutum 30 a ƙauyen Kutunku

Gwamna Bello

Daga UMAR M. GOMBE

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 30 a Litinin da ta gabata a garin Kutunku da ke yankin ƙaramar hukumar Wushishi a jihar Neja.

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya fito ya bayyana cewa daga yanzu babu wata tattaunawa da ‘yan bindigar da ke yin garkuwa da mutane.

Bayanai sun tabbatar cewa ‘yan bindigar sun shiga ƙauyen Kutunku ne ɗauke da makamai kuma a qafa, inda suka yi wa ƙauyen zobe.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun ɓoye baburansu a daji ne sannan suka ƙarasa ƙauyen a ƙasa inda suka yi wa ƙauyan shigar ba-zata.

Majiyar ta ci gaba da cewa bayan sun kwashi mutanen sai suka tafi da su har sansaninsu kuma a ƙasa.

A cewar majiyar mutum 30 ne lamarin ya shafa (maza da mata), ciki har da Gwarawa da Fulani.

Wani ma’aikacin ƙaramar hukumar ya ce an kai batun ga hukumar ‘yan sanda a Zungeru inda ake dakon ji daga gare su. Sai dai, duk qoqarin jin ta bakin ‘yan sanda da wakilinmu ya yi, hakan ya ci tura.

Shugaban ƙaramar hukumar Rafi, Alhaji Ismaila Modibo Kagara, ya tabbatar wa Manhaja faruwar lamarin. Inda ya ce abin tashin hankalin ya auku ne a ƙauyen Kutunku a ƙaramar hukumar Wushishi mai maƙwabtaka da Yakila a qaramar hukumar Rafi.

Modibo ya ce ko a makon da ya gabata, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mutum 18 a Kundu wanda har zuwa wannan lokaci ba a ji komai daga gare su ba.

Sai dai Gwamna Sani Bello ya ɗauki matakin ƙarfafa ‘yan bijilanti na jihar da kayayyakin aiki don su yaƙi ‘yan bindigar waɗanda ya kira da maƙiyan alm’umma. Tare da cewa daga yanzu babu sauran tattaunawa da ‘yan bindigar.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*