Neja: Bello ya tabbatar da sace ɗalibai 27 da wasu mutum 15 a yankin Kagara

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da ‘yan bindiga sun sace ɗaliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara su 27 da ma’aikatar makarantar 3 da kuma wasu mutum 12, a garin Kagara cikin ƙaramar hukumar Rafi, jihar Neja.

Bello ya tabbatar da faruwar haka ne ga manema labarai a ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala taron gaggawa da shugabannin tsaro a Minna, babban birnin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa ‘yan bindigar sun shiga makarantar ne da misalin ƙarfe biyu na daren Laraba, inda suka kashe ɗalibi guda da sace ɗalibai 27 tare da ma’aikatan makarantar su 3 da kuma wasu mutum 12.

Bisa wannan dalili ne gwamnan ya bada umarnin gaggawa kan a rufe dukkan makarantun kwana da ke yankin Shiroro da Rafi da kuma Muyan har sai lamurra sun daidaita.

Ya ce, “Ina kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su ƙyamaci dukkan nau’uka na muggan laifuka a jihar”

Haka nan, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da hanyoyin da suka yassara gare ta wajen kare jihar, yayin da ita kuma gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin abin da ya dace domin kuɓutar da ɗalibai da ma’aikatan da aka yi garkuwa da su.

Gwamna Bello ya ƙara da cewa, babu wata fansa da Gwamnatin Jihar za ta biya ‘yan bindigar don kuɓutar da mutanen da suka kwashe, amma cewa a shirye gwamnati take ta karɓi duk wani ɗan bindiga da ya shirya tuba ya miƙa makaminsa.

Yana mai cewa, “Duk lokacin da ka nemi sulhu da biyan fansa ga ‘yan bindiga, za su yi amfani da kuɗin ne wajen sayen ƙarin makamai.”

Binciken NAN ya gano Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara na da adadin ɗalibai 650, inda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da ɗalibai 27 tare da kashe ɗalibi guda mai suna Benjamin Doma.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 14 ga wannan wata ne ‘yan bindiga suka sace wasu matafiya su 40 a kan hanyarsu ta zuwa Minna bayan sun baro Kontagora. Kodayake dai 8 daga cikinsu sun kuɓuta, yayin da ragowan na hannun ‘yan fashin dajin.