
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗalibai daga kimanin jami’o’in gwamnati guda 23 da wasu makarantun polytechnics sun koka game da jinkiri da aka samu bisa karɓar rancen kuɗi daga Asusun bada bashin kuɗin karatu na NELFUND domin cigaba da gudanar da karatukansu cikin sauƙi.
A watan Afrilun 2024 ne Shugaba Tinubu ya sanya hannu ga dokar bada rancen kuɗin karatu ga ɗalibai don ƙarfafa musu gwiwa musamman a mataki na gaba da sekandire.
News Point ta ruwaito cewa ɗalibai da dama ne suka ci gajiyar shirin tun daga ranar 3 watan Fabrairun 2025, inda aƙalla an bada kimanin Naira biliyan 20.07 ga ɗalibai 192,906 cikin 364,042 da suka nemi rancen.
Saidai, duk da cewa NELFUND ya wallafa bayani a shafinsa na X game da lamarin, ɗalibai daga jami’o’i da dama sun koka da rashin samun rancen zuwa wannan lokaci.
Sun bayyana cewa na ba da jimawa ba za a rufe shafukan rajista, ga kuma jarrabawa da ke ƙaratowa, kamar yadda wasu suka wallafa a shafukan sada zumunta.
Wani jami’in NELFUND da ya buƙaci a sakaye sunansa ya ɗora laifin rashin tura kuɗaɗen akan makarantun ɗaliban, duk da cewa bai bada cikakken bayani game da hakan ba.