NESG ta nemi ƙaruwar mata a harkokin siyasa da noma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasa ta Nijeriya (NESG), ta nemi a ƙara shigar da mata cikin harkokin siyasa da noma don ƙara ƙaimi ga cimma muradun cigaba mai ɗorewa a ƙasar.

Dokta Osasiyi Dirisu, Mataimakiyar Darakta a Cibiyar Innovation Policy, NESG, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani taron manema labarai kan bugu na farko na Cibiyar Innovation Center (PIC) Gender and Inclusion Summit (GS-22) a Abuja.

Dirisu ta ce, shigar da mata a fagen siyasa da kuma harkar noma zai taimaka wajen cimma manufofin SDG da inganta haɗa jinsi.

Ta ce, babban taron da za a yi zai samar da wata kafa da za ta binciko hanyoyin kawo sauyi don inganta haɗa kai, daidaito da kuma samar da tsarin tafiyar da harkokin jinsi a ƙasar.

“Mun fahimci cewa mata ba su da wakilci a siyasa kuma mun sadaukar da hanya guda don tabbatar da tattaunawa a taron,” inji ta.

Ta ci gaba da cewa, idan mata sun shiga siyasa mai ma’ana akwai buƙatar sauya tunani, kawar da shingayen da ke shafe su da kuma bada goyon baya don bunƙasa harkokinsu na siyasa.

“Abin da za mu yi shi ne mu fara tattaunawa, mu gano inda shingaye suke sannan mu yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa.

“To mene ne hujjar abin da ke hana su shiga cikin tsarin siyasa? Muna buqatar fara gano wannan, haɗa shi tare, duba irin dabarun manufofin za su iya taimakawa.

“Wannan shine dalilin da ya sa ɗaya daga cikin manufofinmu shine inganta tsarin tafiyar da harkokin jinsi, idan ba mu da wannan a wurin, ba za mu iya ginawa a kan wannan tushe ba, ko kuma mu fara magana game da shigar da mata a siyasance a cikin siyasa,” inji ta.

Har ila yau, Mista Laoye Jaiyeola, babban jami’in ƙungiyar (Shugaba), ya ce, rashin daidaiton jinsi ya shafi mata.

Jaiyeola ya danganta ƙarancin shigar mata a harkar noma da rashin isassun kuɗaɗe da tallafi.

“Gaskiyar lamarin ita ce, idan aka zo batun duk wani ƙari da kuma duk abubuwan da ke da ƙarin sanarwa da kima, mata ba sa shiga.

“Don haka a matsayinmu na al’umma, idan da gaske muka inganta shigar da jinsi tare da inganta shi, zai nuna cewa wannan tattalin arzikin zai yi mana kyau sosai,” inji shi.

Sai dai ya yaba wa gwamnatin Nijeriya bisa aiwatar da manufofi irin su National Gender Policy, National Gender Action Plan (NGAP) da nufin inganta haɗa jinsi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *