Netanyahu ya naɗa sabon Jakada ga Amurka kwanakin kaɗan bayan Trump ya lashe zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya naɗa Yechiel Leiter a matsayin Jakadan ƙasar ga Amurka.

Leiter, wanda haifaffen Amurka ne, ya kasance shi ne shugaban ma’aikatan Ma’aikatar kuɗi.

Ya kuma riƙe muƙaman mataimakin Darakta-Janar na Ma’aikatar Ilimi da kuma shugaban riƙon ƙwarya na Kamfanin Tashoshin Jiragen ruwa na Isra’ila.

Hallau, an kashe masa ɗansa a shekarar da ta gabata a yaƙin Gaza da dakarun Hamas, a matsayinsa na sojan Isra’ila.

Netanyahu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce Leiter masani ne a harkar difulomasiyya, ƙwararren kakaki kuma wanda ya san siyaysa da al’adun Amurka.

Hakan na zuwa ne kwanaki uku bayan zaɓan Donald Trump a matsayin shugaban Amurka karo na biyu da ƴan ƙasar suka yi.