Daga USMAN KAROFI
Kamfanin Netflix ya musanta rahotannin da ke cewa zai bar kasuwar Nijeriya, inda ya jaddada ƙudurinsa na cigaba da zuba jari a masana’antar fina-finai ta ƙasar. Wannan karin haske ya biyo bayan rahotannin da suka yaɗu bayan jawabin wani shahararren ɗan fim, Kunle Afolayan, a lokacin bikin Zuma International Film Festival na 2024.
Afolayan ya bayyana cewa Netflix ya soke wasu ayyukan da wasu masu shirya fina-finai suka gabatar kwanan nan, wanda ya sa ake tambayar makomar kamfanin a Najeriya. “Lokacin da muka sanya hannu kan yarjejeniyar fim guda uku da Netflix shekaru uku da suka wuce, lokaci ne na farin ciki,” in ji Afolayan.
Tun bayan shigowarsa Nijeriya a 2018, Netflix ya kasance abokin tarayya ga masana’antar Nollywood, yana taimakawa wajen yaɗa fina-finai na gida zuwa ga masu sauraro na duniya. Kamfanin ya tabbatar da cewa zai cigaba da aiki tare da masana’antar fina-finai don samar da ingantattun ayyuka masu kyau da inganci.