Daga SANUSI Muthammad a Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da tsarin rabon kuɗaɗe ba tare da wani sharadi ba ga mutane 44,000 za su ci gajiyar shirin a ƙarƙashin ayyukan Bankin Duniya, wato NG-CARES.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin da aka gudanar a Sakatariyar JB Yakubu dake Gusau, a ranar Talata, Gwamna Dauda ya bayyana cewa shirin na da nufin inganta rayukan al’ummar jihar.
A cewarsa, shirin ya kasu kashi uku inda aka zaɓo dukkan wadanda suka ci gajiyar shirin cikin tsanaki a ƙananan hukumomi 14 dake jihar.
Ya yi nuni da cewa, a ƙarƙashin tsarin jin-daɗin al’umma na ‘Cash transfer, waɗanda za su ci gajiyar shirin za a ba su N20,000 a kowane wata na tsawon shekara ɗaya.
“Domin tabbatar da daidaiton jinsi, kashi 60 cikin 100 na waɗanda suka amfana mata ne, da suka ƙunshi, waɗanda suka rabu da mazajensu, matan aure, ƴan mata masu ƙananan sana’o’i da sauransu,” inji gwamnan.
Ya kuma ƙara da cewa a ƙarƙashin tsarin, waɗanda suka ci gajiyarsa, za a riƙa ba su N10,000 kowane wata a matsayin alawus na tsawon shekara ɗaya a tsakanin masu fama da nakasa.
N150,000 za a ke bai wa kowane ɗaya daga cikin ƙananan ƴan kasuwa don bunƙasa harkokinsu.
Har’ilayau, gwamna ya ce za a bayar da N50,000 ga “Ƴan agaji, malamai a makarantun Islamiyya da sauransu don inganta rayukansu.”
Ya kuma yaba da goyon bayan da sarakunan gargajiya suka ba gwamnatinsa domin samun nasara, inda ya yi kira ga mutanen da suka amfana da shirin da su yi amfani da abin da aka ba su yadda ya kamata.
“Ku tuna an baku waɗannan kuɗaɗen ne don ku gina kanku, kar ku samu kuɗin ku je kuce aure zaku yi da su, amma ku yi amfani da su yadda ya kamata.”