NGF ta yi kira da a sake duba dokar albarkatun ruwa ta ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta yi kira da a sake duba ƙudirin dokar albarkatun ruwa ta ƙasa domin daidaita matsalolin da ke damun jihohi.

Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Laraba a Abuja kuma mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti bayan wani taron wayar da kai a ranar Talata.

Fayemi ya ce, ƙudurin dokar da aka sake dawo da shi bai yi daidai da muradun jihohi ba kuma ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, taron ya samu bayanai daga Ministan Noma da Raya Karkara, Dr Mohammad Mahmood Abubakar, kan shirin samar da aikin noma da karko na dabbobi (LPRES) – shirin na dala miliyan 500 na bankin duniya na shekaru 6.

Shirin an yi shi ne don inganta haƙƙin haɓaka kiwo da kasuwanci da juriya na tsarin kiwon dabbobi da aka yi niyya a Nijeriya.

Fayemi ya ce, gwamnonin baki ɗaya sun amince su jagoranci shirin a jihohinsu.

Wannan, a cewarsa, musamman a fannonin da suka haɗa da inganta tsarin cibiyoyi da na zamani, inganta sarƙar qimar dabbobi, rigakafin rikice-rikice da magance rikice-rikice da daidaita ayyuka.

Ya ƙara da cewa, Ministar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta Ƙasa, Misis Zainab Ahmed ta gabatar da daftarin 2023 – 2025 kan matsakaita (MTEF) da manyan ayyukan (FSP). da ya kamata a aiwatar.

Fayemi ya bayyana cewa, gabatar da shirin na daga cikin hanyoyin tuntuvar juna wajen bunƙasa manufofin gwamnatin tarayya na kasafin kuɗi.

Har ila yau, ya kasance don raba ra’ayoyin tattalin ariki da kasafin kuɗi masu dacewa don taimakawa Jihohi don shirya Tattalin Arziki da Kuɗi (EFU), FSP da Bayanin Manufofin Kasafin kuɗi (BPS).

“Bayan gabatarwar, gwamnoni sun yi tattaunawa mai ƙarfi tare da fifikon mayar da martani ga gwamnati game da abubuwan da suka faru na yaqin Rasha da Ukraine (ciki har da hauhawar farashin kaya da tashin hankali na abinci da abinci).

“Ci gaba da tasirin tallafin man fetur a babban dakin kasafin kuɗi na gwamnatoci, tasirin sabon canjin da kamfanin NNPC ya yi kan kuɗaɗen shiga na tarayya.

“Bambance-bambancen da ke tsakanin hukuma da daidaitattun kasuwannin dala akan kuɗin,” inji shi.

Fayemi ya ce, shirin jihar Action on Business Enabling Reforms (SABER) shi ma Dr Jumoke Oduwole, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sauƙin kasuwanci ya gabatar da shi.

SABER wani shiri ne na tsawon shekaru 3 wanda ƙungiyar fasaha ta Bankin Duniya da Sakatariyar PEBEC suka tsara tare da tallafi daga Ma’aikatar Kuɗi da Tsare-tsare ta Tarayya (FMFBNP), Sashen Kuɗi na Gida (HFD) da Sakatariyar NGF.

Wannan ya kasance don ƙarfafawa da aiwatar da sauye-sauye na kasuwanci a faɗin Nijeriya.

SABER ya kasance magajin fasaha ga Fahimtar Kuɗi na Kasafin Kuɗi na Jiha, Bayar da Lamuni da Ɗorewa (SFTAS).

“A bisa manufofin shirin, dandalin ya amince da shirin tare da ƙuduri aniyar kafa wani kwamitin wucin gadi da zai jagoranci aiwatar da shirin a dukkan Jihohin ƙasar nan.

“Don ci gaba da cimma manufofin Sanarwa, taron ya himmatu wajen tattara ƙungiyoyin jihohinsu da na ƙananan hukumomi don ƙalubalen Jagorancin PHC.

“Takamaiman alƙawurra sun haɗa da cewa za a magance ayyukan kiwon lafiya na farko (PHC) a matakin majalisar zartarwa na jiha, gwamnoni za su gudanar da ziyarar wuraren PHC.

“Gwamnoni za su yi taro da shugabannin gargajiya don tattaunawa kan PHC, mataimakan gwamnoni za su jagoranci kwamitin PHC, yayin da za a kafa kwamitocin Jihohi kan abinci mai gina jiki,” inji shi.

Fayemi ya bayyana cewa, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya yi jawabi a taron kan tallafin Asusun Duniya ga gwamnatocin jihohi da aka tsara don gyara cibiyoyin kiwon lafiya na farko, Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Jiha, Ayyukan Ambulance da Tallafin Gudanar da Magunguna a Jihohi.

Ya ce, bayan haka gwamnonin sun yanke shawarar yin aiki tare da ma’aikatar lafiya ta tarayya don aiwatar da shirin.

Fayemi ya kuma ce taron ya samu gabatarwa daga shugabannin Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta ƙasa (NPHCDA) kan asusun ƙalubalen jagoranci na kiwon lafiya a matakin farko.

Asusun ya samo asali ne daga Sanarwa na Seattle – Tsarin Kiwon Lafiya na Farko da Ci gaban jarin Ɗan Adam wanda Bill Gates, Alhaji Aliko Dangote, mataimakin shugaban zagaye da NGF suka shirya a watan Nuwamba 2019.

“Sanarwar Seattle ta tsara jerin alƙawurra ga gwamnatocin Jihohi gami da aiwatar da Kiwon Lafiya na Farko a ƙarƙashin Rufi ɗaya, Kunshin Sabis mafi ƙarancin farashi wanda aka keɓance ga Jihohi.

Bukatun Asusun Kula da Kiwon Lafiya na Jiha, ingantattun kuɗaɗe ga PHC kamar yadda Kwamitin Abuja ya tanada; “Bita kan ayyukan PHC na Jihohi a Majalisun Zartarwa na Jihohi, kwamitin haɗin gwiwa kan PHC ƙarƙashin jagorancin mataimakan Gwamnoni, da yadda shugabannin gargajiya da na addini suka yi aiki a kan PHC,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *