Ngozi Iweala ta shiga jerin fitattun mata 25 na duniya

Daga AISHA ASAS

Haifaffiyar Nijeriya, kuma ‘yar ƙabilar Ibo, Ngozi Okonjo-Iweala, ta cira tuta a jerin matan Nijeriya ta hanyar zama ɗaya daga cikin fitattun mata 25 da suka yi suna tare da taka wata muhimmiyar rawa a duniya.

Fitacciyar Jaridar kasuwanci ta duniya ce ta bayyana hakan wato ‘Financial Times’.

Okonjo-Iweala wadda ta kasance babbar darakta ta Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, ta zama ta farko a jerin sunaye 25 na fitattun mata masu faɗa a ji a duniya, duk da cewa jaridar ta ‘Financial Times’ ta bayyana cewar, ba sun fitar da jerin sunayen ne bisa fifiko ba.

FT ta ƙara da cewa, “mun tattara sunayen ne tare da haɗin gwiwar dubban ‘yan jaridunmu da ke lungu da saƙon ƙasashen duniya, ta hanyar zaƙulo sananu cikin mata kai har ma da matan da ba su shahara ba.”

Jaridar ta ƙara da cewa, “matan sun kasance daga nahiyoyi da dama, kuma sun taka muhimmiyar rawa tare da ba da gudunmawa ga ci-gaban al’umma.”

Shugabar Babban Bankin Nahiyar Turai Christen Lagarde, ta bayyana Okonjo a matsayin jaruma kuma mai hangen nesa.
Ta kuma ƙara da cewa, “na san Ngozi tun shekarar 2005, kuma na sha ganin yadda ta ke warware matsalolin da ke tasowa, tare da sulhu tsakanin mutane cikin ƙwarewa.”

“A shekaru 25 da ta yi a Babban Bankin Duniya, ya bayyana ƙwarewarta kan warware matsalolin tattalin arziki da kuma yunwa da ta ke addabar wasu qasashen duniya, musamman rawar da ta taka a shekarar 2008 zuwa 2009. Tabbas ta cancanci yabo ko ta ɓangaren tsayin daka da ta yi na ganin an dawo da ƙadarorin da aka sace.”

Christen ta bayyana Iweala a matsayin mace mai kamar maza, wadda ta taka rawar da ba macen da ta taɓa takawa a Nijeriya da Afirka bakiɗaya. Inda ta ke cewa, ” ita ce mace ta farko da ta riƙe ministan kuɗi da ministan harkokin waje a Nijeriya. Ta riƙe waɗannan muƙamai bisa ƙwarewa da bayyanar da gaskiya, wanda ya kai ta ga zama mace ta farko a Afrika da ta shugabanci Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya.”

Jerin sunayen da aka fidda sun haɗa da:
1 – Ngozi Okonjo-Iweala
Babbar Darakta ta Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya

2 – Lina Khan
Shugabar Hukumar Ciniki ta Ƙasa

3 – Mary Barra
Shugaba kuma mammalakiyar ‘General Motors’

4 – Gita Gopinath
Babbar masaniyar tattalin arziki, IMF

5 – Luiza Trajano
‘Yar kasuwa kuma mai taimakon jama’a

6 – Nancy Pelosi
Kakakin Majalisar wakilai ta Amurka

7 – Mariam Al-Mahdi
‘Yar siyasa, Sudan

8 – Kate Bingham
Tsohuwar shugabar UK Vaccine Taskforce

9 – Cathie Wood
Wadda ya kafa kuma shugaba ta Ark Investment Management

10- Rosalind Brewer
Shugabar, Walgreens Boots Alliance

11- Tsai Ing-Wen
Shugabar Taiwan

12 – Frances Haugen
Masaniyar kimiyyar bayanai kuma mai fallasa

13 – Naomi Osaka
‘Yar wasa

14 – Elisa Loncón Antileo
Shugabar, Chile’s Constitutional Convention

15 – Agnes Chow
‘Yar gwagwarmayar dimokraɗiyya

16 – Liz Cheney
‘Yar Majalisar wakilai ta Amurka

17 – Vanessa Nakate
Lauyan Adalci

18 – Sotooda Forotan
Ɗaliba kuma ‘yar gwagwarmaya

19 – Sviatlana Tsikhanouskaya
Shugabar Majalisar Gudanarwa ta Belarus

20 – Chloé Zhao
Mai shirya fina-finai

21 – Sally Rooney
Marubuciya

22 – Shonda Rhimes
Shugabar Mai shirya shirin talabijin, marubuciya kuma mai rubutu fim

23 – Scarlett Johansson
Jaruma

24 – Paula Rego
Mawaƙiya

25 -Gabriela Hearst
Daraktan Ƙirƙira ta Chloé; Founder kuma Daraktan Ƙirƙira ta Gabriela Hearst