Ni ba Rahama Sadau ba ce- Teema Makamashi

Daya daga cikin fitattun jarumai a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood FATIMA ISAH MUHAMMAD wadda aka fi sani da Teemah Makamashi, ta bayyana harkar fim a matsayin wata harkar da ta yi mata rana, domin kuwa kamar yadda ta bayyana wa wakilin mu a lokacin da ya tattaunawa da ita dangane matsayin harkar fim a gare ta. Haka kuma jarumar ta yi tsokaci game da dambarwar Kannywood na Rahama Sadau. Ga yadda hirar ta kasance tare da wakilin mu ALIYU ASKIRA:

“Harkar fim ta yi mini rana, saboda ita ta yi mini wando har da riga da bargon da na ke rufa, saboda a cewar ta dalilin fim ne Duniya ta sanni da har na samu matsayin da na samu kaina a ciki, don haka a yanzu sai dai na yi godiya ga Allah kan ni’imar da ya yi mi ni ta dalilin wannan harkar ta fim.”

 Ta ci gaba da cewar” ita harkar fim sana’a ce da take da kima ba kamar yadda wasu su ke kallon ta ba, don haka duk wanda ya shigo harkar fim domin ya yi sana’a ya samu kudin da zai rufa wa kan sa asiri, to shi ne kullum za ka ga yana samun cigaba, don haka da an shigo ta ne domin neman arziki ba wai don wasa ba. Ka ga kuma a yanzu Alhamdulillah na samu cigaba a rayuwa ta fiye da yadda a ke zato.”

Dangane da yadda ta fara harkar kasuwanci banda harkar fim kuwa?

Teemah Makamashi cewa ta yi duk da wasu na kallon kasuwancin da ‘yan fim su ke yi a yanzu na yayi ne, ta ce, “Ni a gaskiya ba don yayi na fara kasuwancin da na ke yi ba, daman can tun kafin na bude wajen da na ke a yanzu ina yin kasuwanci a Soshiyal Midiya, don haka ko da na bude waje na qara bunqasa shi ne, kuma abin farin ciki tun daga bude wajen da na yi zuwa yanzu na samu alheri mai yawa domin ta dalilin hakan na qara sanin mutane da yawa fiye da yadda nake a baya, don haka arziki sai qaruwa ya ke yi, sai godiyar Allah”.

Mun tambaye ta ko harkar kasuwancin ta zai ba ta damar ta ci gaba da fitowa a finafinai kuwa?

Sai ta ce “Babu abin da zai hana domin a yanzu ma ina cikin harkar fim kasuwanci na ba zai hana ni ba, saboda a ta dalilin fim na kawo matsayin da na ke, don haka fim sana’a ta ce da duniya ta sanni da ita kuma har gobe ina cikin ta. Sai dai abin da na ke so mutane su sani ita harkar fim ta na da lokaci, amma shi kasuwanci ba shi da lokaci. Abin da na ke nufi shi harkar fim za ka tsufa, ko a daina yayin ka, ko ka yi aure, amma shi kasuwanci za ka iya yi har ma ‘ya’yan ka su gada, don haka harkar fim tana da iyaka da lokaci, amma shi kasuwanci ba shi da iyaka ba shi da lokaci, don haka a yanzu ka ga na bude shago wanda na ke sayar da Shaddodi da yaduka takalma agogo atamfa da sauran kayayyaki na ado, kuma ina da yara da su ke samun arziki ta qarqashin wannan kantin nawa, don haka sai dai godiya ga Allah da ya kai ni ga wannan matsayin, amma dai ina da burin nan gaba kasuwanci na ya bunqasa har na fi Dangote ma, don haka buri na mai tsawo ne a harkar kasuwanci.

 Ta yi kuma kira ga mata da su tashi su nemi na kan su ta hanyar sana’a da kasuwanci, kuma ba wai sai an yi burin fara kasuwancin da kudi mai yawa ba, komai qanqantar kudi idan aka fara kasuwanci da su idan da kyakyawar niyya sai Allah Ya sa albarka a cikin lamarin don haka mata musamman ‘yan fim ku rinka hadawa da kasuwanci, domin ita ce hanya mai dorewa, wadda ba a daina yayin ta. In ji Teemah Makamashi.

Me ki ka fi tsana a rayuwar ki?

Qarya da rashin gaskiya, idan ka san baka da gaskiya, kar ma ka zo wajen Teema Makamashi domin ba ni da lokacin maqaryata da ma yaudara, ko addinin musulunci ya haramta qarya da yaudara saboda haka, ko a yaushe ina yin qoqari in ga cewa ban yi wa kowa qarya ba.

 Rikicin da ya taso a Kannywood a kwanan nan na Rahama Sadau, me za ki ce?

Kowa da yadda yake so ya yi nashi rayuwar, kuma abin da ya faru ni bai shafe ni ba kuma bazai hana ni in ci gaba da harkan fim ba domin ni daban, da sauran matan, sunana Fati Isa Makamashi sauran kuma suna da sunayen su daban-daban, to ka ga halin mu ba zai zama daya ba, kuma zargi da ake mana mu ‘yan fim wai muna shaye-shaye da wadansu halaye na banza, wallahi koma ina ka je a yau zaka tarar da irin wadannan mutanen, mu ne dai duniya ta fi sa mana ido.

 Maganar aure fa?

Na tava yin aure a baya kuma buri na ma shi ne Allah ubangiji ya kawo mini mutumin kirki in aura, amma kafin Allah ya yi ikon sa, ina nan kan harkata ta fim da kasuwanci.