Ni ke zuwa ta ƙarshe a duk lokacin da aka yi jarrabawa a makaranta, cewar jaruma Toke Makinwa

Daga AISHA ASAS

Shararriyar jaruma kuma sananniyar ‘yar soshiyal midiya, Toke Makinwa ta bayyana kanta amatsayin wadda ba ta bar abin a yaba ba alokacin da take makaranta.

Jarumar ta bayyana cewa, a cikin ɗalibai 52, ita ke zuwa ta karshe a duk lokacin da aka yi jarrabawa.

Toke ta bayyana wannan ɓoyayen lamari game da rayuwarta wanda ba kasafai mutane ke iya faɗar rashin ƙoƙarin da suka yi a makaranta ba, asalima ire-iren waɗannan mutane sun fi ɓoye wannan ɓangare na rayuwarsu musamman ma ga ‘ya’yansu.

A cewar jarumar, “A kullum aka yi jarrabawa ni ke rufe aji, a cikin ɗalibai 52, ni ke zuwa ta 52. Akwai wata rana da na zo ta ƙarshe, wato 52, sai na cire 5 ɗin na bar 2, wanda a lokacin ina kallon kaina a matsayin mai dabara.

Sai dai a lokacin da na je gida, na nuna wa mahaifana, ina alfahari da hakan, inda na samu cirawa daga zama ta ƙarshe zuwa ta biyu, amma maimakon abinda nake tunani, wato yabawa sai suka yi min duka.

Mahaifiyata ba ta bar ni ba, har sai da na ji kunyar abinda na aikata. Duk da hakan wannan matar (mahaifiyata) ba ta taɓa fitar da rai kaina ba, kuma ta yarda da zan iya. A haka take tada ni tsakiyar dare don in yi karatu.

Mama na san ni ke zuwa ta karshe a makaranta, amma a yau, Mama na ƙaddamar da turare na kaina.”