Ni na kashe Ummita amma ba da gayya ba, inji Ɗan Chana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan ƙasar Chanan nan mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 da ake tuhuma da laifin kashe budurwarsa (Ummita) a jiya Alhamis ya tabbatar wa wata babbar kotu a Kano cewa ya dava wa budurwarsa ‘yar Nijeriya mai suna Ummukulsum Sani wadda aka fi sani da Ummita wuƙa, amma ba da niyyar kashe ta ba, a cewarsa.

Wanda ake tuhumar, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, na ci gaba da gurfana ne a gaban kotun bisa laifin kisan kai.

Frank da lauyan masu gabatar da ƙara ke yi masa tambayoyi, Darakta mai shigar da ƙara na jihar Kano, DPP, Aisha Mahmoud, ya shaida wa kotun cewa a wannan ranar da ibtila’in ya afku, abubuwa da dama sun faru.

Ya shaida wa kotun cewa ya zo Nijeriya ne a shekarar 2019 domin yin aiki a matsayin Manajan Kasuwanci da Tallace-tallace a kamfanin BBY Textile Kano.

“Ana biyana Naira miliyan 1.5 duk wata kuma ina yin wasu sana’o’in daban-daban. A ranar ƙaddara Ummukulsum ta tura ni kan gado.

“Na caka mata wuqa ne ba tare da niyyar kashe ta ba.

“Na fita daga ɗakin ta taga tunda an kulle ƙofa daga waje ina so in kai Ummukulsum asibiti amma sai ‘yan sanda suka iso suka kama ni,” in ji Mista Frank.

Lauyan da ke kare, Muhammad Dan’azumi, ya gabatar da wani likita, Dokta Abdullahi Abubakar, a matsayin shaida na biyu (DW2).

Ku tuna a baya Mista Frank ya shaida wa kotu cewa Ummukulsum ta raunata shi a al’aurarsa.

Abubakar ya shaida wa kotun cewa ya shafe shekaru sama da 30 yana aikin likitan mata, kuma ya shafe shekaru 13 yana koyarwa a asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda ya bada wasu shaida dangane da lafiyar mazakuta da kuma abinda zai iya faruwa idan aka raunata ta.

Mahmoud ya yi zargin cewa wanda ake ƙara a ranar 16 ga Satumba, 2022 ya dava wa marigayiyar wuqa a gidanta da ke Janbulo Quarters Kano.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

A cewar mai gabatar da qara, laifin ya ci karo da tanadin sashe na 221(b) na kundin laifuffuka.

Mai shari’a Sanusi Ado-Ma’aji, bayan sauran bayanai daga lauyan da ke kare wanda ake ƙara da kuma shaidu da bayanan likita, sai ya dage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 6 ga Afrilu, domin yi masa tambayoyi da kuma ci gaba da kare shi.