Ni ne halastaccen ɗan takarar Sanata a Kano ta Tsakiya a NNPP ba Shekarau ba – Hanga

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce har yanzu shi ne halastaccen ɗan takara a Kano ta Tsakiya na jam’iyyar duk kuwa da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta yi kuskuren sanya sunan Sanata Shekarau a jadawalin sunayen wanda da shine ke takarar kafin ficewarsa daga jam’iyyar.

Sanata Hanga ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Kano, inda ya ce hankalin magoya baya ya tashi akan kuskuren da aka samu a sunayen da hukumar zaɓen ta fitar, domin Shekarau shine wanda jam’iyya ta bayar da farko kafin lokacin da ya rubuta wa jam’iyya cewar ya bar ta ya rubutawa INEC takarda ya ce ya fita daga zaɓe, bisa ƙa’ida ba dama hukumar zaɓe ta cire sunansa sai an je kotu.

Ko a fito da sunaye na kwanan nan da hukumar zaɓen ta yi ai ta rubuta a ƙasa cewa duk wata jam’iyya da ta ga akasin matsayinta a yanzu ta rubuta mata sannan ta je ta yi rantsuwa a kotu. A bisa ƙa’ida idan INEC ta yi aiki ba mai ce mata ga yadda doka ta tanada sai kotu kuma in an je kotu za a warware komai.

Ya ce: “Jam’iyyar NNPP ta rubuta kuma su inda Allah ya taimake su sun zo an yi zaɓen fidda gwani kafin lokaci ya ƙure har lokacin an tura wasu ma su kawo hayaniya don su hana da rannan ba a yi ba shi kenan ta wuce su, amma sai bayan an yi an gama suka tada hargitsi.

Hanga ya ce Jam’iyyar NNPP ta kai sunansa ga INEC saboda haka yanzu an kai kotu akwai wasu jam’iyya su ma an yi haka sun kai kotu har hukumar zave ta mai da sunayensu.

Ya ce suma ranar biyar ga watan 10 kotu za ta zauna akan nasu domin a dokar zaɓe akwai sashe 31 ya tanadi cewa duk inda mutum ya ce baya takara ko ya rasu za a sauya shi.

A jerin sunaye ma da INEC ta buga ba ma wanda ya ce ba ya yi kamar Shekarau ba har wanda ya rasu an sanya sunansa, ba za su canza ba sai an je kotu za su ce wane ya mutu za su canza da wani, inji shi.

Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce akwai ‘yan takara da suka mutu a wasu jihohin da waɗanda suka janye duk an buga sunansu kuma duk za a canza, saboda haka a cewarsa wannan ba matsala ba ce.