Ni ne zan yi nasara a zaɓen Gwamnan Katsina – Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya ce yana da yaƙinin shi ne zai lashe zaɓen jihar.

Raɗɗa ya bayyana haka ne ranar Asabar jim kaɗan bayan da shi da mai ɗakinsa, Hajiya Zulaihat suka kaɗa ƙuri’arsu a mazaɓar Katuka mai lamba 010 da ke mahaifar ɗan takarar dake Ƙaramar Hukumar Charanci ta jihar Katsina.

A zantawar da ya yi da manema labarai, Raɗɗa ya ce, “Na zo don kaɗa ƙuri’ata a matsayin haƙƙin ɗan ƙasa.

“Ina fata zaɓen zai samar wa al’umar Jihar Katsina shugaba nagari, don haka dole in gode wa Allah a kan haka.

“Muna da tabbacin ni zan yi nasara ta yadda Jihar Katsina za ta samu sabon shugabanci, insha Allah,” Inji shi.

A cewarsa, jihar na buƙatar samun canji da ƙaruwar bunƙasa ta fannoni daban-daban, don haka ya ce shi ne wanda iya cire wa jihar da alummarta kitse a wuta.

Ya nuna gamsuwarsa dangane da yadda mutane suka fito don kaɗa ƙuri’arsu da kuma yadda na’urar tantance masu zaɓe ke aiki ba tare da wata matsala ba.