Nijar ta yanke alaƙa da maƙwabciyarta Nijeriya

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin sojijin juyin mulki, ta sanar da yanke alaƙa da Nijeriya bayan da ƙoƙarin ECOWAS na samar da maslaha a ƙasar ya ci tura.

ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulkin wa’adin mako guda a kan su maida Mohamed Bazoum kan kujerarsa ko kuma a yaƙe su da ƙarfin soji.

A ranar Alhamis da ta gabata Shugaba Bola Tinubu a matsayinsa na Shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya tura tawaga ta musamman ƙasar Nijar domin tattauna maslaha.

Tawagar ta tafi Nijar ɗin ne ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) inda ta gana fa wakilan sojojin ƙasar.

Bayanai daga ƙasar sun ce baya ga Nijeriya, ƙasashen Togo da Faransa da Amurka na daga cikin ƙasashen da dangantakarsu da Nijar ts yi tsami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *