Nijeriya ƙasarmu ta gado!

Daga YUSUF MUHAMMAD DOSARA

Yau ma zan sake yin magana a kan wani abu da yake faruwa a jihar Zamfara da ma wasu sassan Nijeriya.

Na ji wani sautin murya na waya da aka yi da ƙasurgumin ɗan ta’addan nan Bello Turji a kan harin da jami’an tsaro suka kai masa a kwanan nan.

Yana ƙorafin cewa wai an yaudare shi an ci amanarsa, an yi sulhu da shi, amma an dawo an farmake shi, an kashe mai mutane kuma an ƙone masa gida.

Wannan maganar ni a wajena babu wani kuskure ko kuma rashin adalci a kan wannan farmakin da aka kai ma wannan ɗan ta’addan.

Amma abun dubawa a nan, kuma abun tsoro a nan shi ne, an kai masa farmaki, amma ba a samu damar kashe shi ba yana nan a raye. Shin wanne hali ake tunanin al’ummar wannan yanki za su shiga?

Shin gwamnati ta san suna da ƙarfin farmakar wannan ɗan ta’addan? Me ya sa tun shekarun da aka baro ba su yi ba sai yanzu da aka yi sulhu ana tunanin an zauna lafiya?

Kuma idan farmakin nasu na gaske ne, menene amfanin hukumar dake kula da kiraye kirayen wayoyi ta Nijeriya ina aikin da suke cewa suna yi?

A ce ƙasurgumin ɗan ta’adda kamar Bello Turji ya kira waya a yi fiye da minti talatin (30) ana waya da shi, kuma yana faɗar cewa, zai kai hari, amma babu wani mataki da aka ɗauka har ya gama wayar. Kuma gobe ya sake babu wani mataki da aka ɗauka a kai.

Ina kira ga gwamnati tun daga kan gwamnatin Tarayya har zuwa ta ƙaramar hukuma, Dan Allah a duba halin da al’ummar wannan yanki za su iya shiga. Saboda na ji wannan ƙasurgumin ɗan ta’addan yana cewa, a kira shi bayan wata ɗaya a ji labari.

To don Allah, kamar yadda kuka fara wannan faɗan, ku tsaya ku yi yadda ya dace domin kare rayuwa, lafiya da kuma dukiyoyin jama’a.

Mu kuma muna rokon Allah S.W.T Sarki, mai kowa mai komai, Sarkin da baya buƙatar komai a wajen kowa, amma kowa nada buƙatar komai a wajensa, ya Allah ka kawo mana qarshen wannan ta’addancin a jihar Zamfara da ma ƙasa bakiɗaya.

Ya Allah ka zaunar da ƙasarmu lafiya, Ka bamu dauwamammen zaman lafiya. Ya Allah ka yi mana maganin duk wanda yake son tashin hankalin al’umma.

Yusuf Muhammad Dosara ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi.