Nijeriya @ 61: Wane ne ya ƙirƙiri tutar Nijeriya?

Daga MOHAMMED BALA GARBA

A ranar Juma’ar da ta gabata aka yi bikin cikar shekaru 61 da samun ‘yancin kan Najeriya. Mutane da dama na nuna farin cikinsu a fili ta hanyar ɗaga tutar Najeriyar da raye–raye da kaɗe–kaɗe. Wasu kuma na sanye da fararen riguna waɗanda ke ɗauke da sunayen jihohinsu da kuma rubutun murnar cikar ƙasar shekaru sittin da ɗaya. A bara har da gasa aka gudanar a tsakanin jihohin Arewancin ƙasar na waɗanda suka fi kowa kyan shiga da ƙwalisa a irin wannan ranar. A bisa haka ne, na ga dacewar yi wa ‘yan’uwana (musamman matasa) taƙaitaccen bayani a kan wanda ya ƙirƙiri wannan tutar tamu ta Najeriya, da kuma yadda aka yi ya ƙirƙire ta.

Tabbas, tarihin Najeriya ba zai cika ba, ba tare da an ambaci sunan haziƙin da ya yi amfani da baiwarsa tare da basirarsa ya ɗauki tsawon lokaci wajen ƙirƙirar tutar Najeriya. Tutar Najeriya da muke amfani da ita, wani bawan Allah ne mai suna Michael Taiwo Akinkunmi da ke da shekaru ashirin da uku (23) kacal a wancan lokacin ya ƙirƙire ta; kafin daga bisani a amince da ita a ƙaddamar a ranar 1 ga watan Oktoban 1960.

Gabanin Najeriya ta samu ‘yancin kai, ƙasar tana amfani ne da tutar Birtaniya a ƙarƙashin gwamnatin Turawan mulkin mallaka na Ingila. Har sai a shekarar 1958, lokacin da ake shirye-shiryen miƙa mulki ga ‘yan Najeriya aka fidda sanarwar gasar zana tutar ƙasar. Jama’a da dama sun shiga gasar, inda kowa ya tura irin nasa zanen. A wannan lokacin, Michael ɗalibi ne da ke karatu a Kwalejin Fasaha ta Norwich da ke Ingila, ya shiga gasar, inda ya turo zanen tutarsa izuwa Legas don tantancewa.

Asalin tutar da Michaeal Taiwo Akinkumi ya zana, mai ɗauke da zanen rana.

Bayan tantance ayyukan zanen da aka gabatar kimanin 2,800 na waɗanda suka shiga gasar, a ƙarshe dai alƙalan gasar suka zaɓi nasa mai launin kore da fari da kore. Sai dai kuma asalin zanen da ya aiko na ɗauke da hoton rana a kan farin, wanda alƙalan gasar suka cire a wannan lokacin.

A ranar 1 ga watan Oktoban 1960, ranar da Turawa suka bai wa Najeriya ‘yancin kanta aka ɗaga tutar da Micheal ya zana, wato mai launin kore da fari da kore, yayin da aka sauke tutar Ingila. Ma’anar launin koren da ke jikin tutar Najeriya shi ne noma, wato hakan na nufin Allah ya albarkaci Najeriya da ƙasar noma, yayin da launin farin ke nuni da zaman lafiya a ƙasar. Turawan da suka miƙa mulki ga Gwamnatin Najeriya a wannan lokacin, sun bai wa Micheal kyautar Pan 100 na Ingila.

Wane ne Micheal Taiwo Akinkumi?
An haifi Micheal Taiwo Akinkunmi a ranar 10 ga watan Mayu, a shekarar 1936 a garin Owu ta jihar Ogun. Ya yi karatun firamare a makarantar Baptist Day Secondary Ibadan, ya yi sakandire a Ibadan Grammar School, ita ma a garin na Badun.

Daga nan ne kuma ya samu aiki a sakateriyar gwamnati ta Ibadan, inda ya yi aiki na tsawon wasu shekaru, daga bisani ya tafi ƙasar Ingila domin ƙaro karatu a Kwalejin Fasaha ta Norwich, inda ya karanci fasahar noma. Mista Taiwo ya dawo Najeriya bayan ya kammala karatunsa, inda ya kama aiki a ma’aikatar ayyukan gona. Ya yi ritaya daga aikin gwamnati a matsayin mataimakin darakta.

Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, a lokacin da yake karrama Micheal Taiwo Akinkunmi

A shekarar 2014 Gwamnatin Shugaba Jonathan ta karrama shi da kyautar girmamawa. Yanzu haka Micheal Taiwo Akinkunmi yana zaune a birni Legas tare da iyalansa da ‘yan’uwa da abokan arziki. Wannan shi ne taƙaitaccen bayani dangane da yadda aka ƙirƙiri tutar Najeriya da kuma wanda ya ƙirƙire ta.

A nan nazo ƙarshen wannan muƙalar tawa, ina addu’ar Ubangiji Allah ya ba mu zaman lafiya da ci gaba mai ɗaurewa a ƙasarmu Najeriya, Amin.

Mohammed Bala Garba, ɗalibi ne a Jami’ar Maiduguri. Za a iya samunsa ta waɗannan lambbin 08025552507 / 08069195272.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *