Nijeriya da ƙasashe 12 mafi ci gaba a Afirka

Wani rahoto na baya-bayan nan da Insider Monkey ya fitar ya nuna cewa Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashe 12 da suka fi samun ci gaba a nahiyar Afirka. A cewar rahoton mai taken, “ƙasashe 12 Mafi Cigaba a Afirka”, Afirka na ɗaya daga cikin nahiyoyin da suka fi arziki a duniya wajen samar da albarkatun qasa. Abin ban mamaki kuma, nahiyar na ɗaya daga cikin yankuna mafi ƙarancin ci gaba a duniya.

Ƙasashen da suka shiga jerin sun yi amfani da albarkatun qasarsu wajen inganta tattalin arzikinsu. Irin waɗannan qasashe su ne; Ghana, Zimbabwe, Masar, Maroko, Afirka ta Kudu, Cote d’Ivoire, Tanzania, Senegal, Botswana, Tunisia, Kenya da Namibiya.

Don isa ga rahoton nata, ƙungiyar ta tuntuvi Cibiyar Samar da Fasaha ta Duniya (WIPO) don fitar da ƙasashe mafi ci gaba a Afirka daga cikin ƙasashe 56 masu cin gashin kansu da ke cikin Majalisar Ɗinkin Duniya. Rahoton ya ce, alal misali, Cote d’Ivoire, ta dogara ne a kan noma, kuma tana fitar da kayayyaki irin su koko, zinariya da kuma albarkatun man fetur. Don haka, ta ƙara haɓaka tattalin arzikinta zuwa Dala biliyan 173 na GDP ta fuskar ƙarfin ƙasa.

Wata ƙasa, Namibiya, ko da yake ƙaramar ƙasa ce mai tattalin arzikin Dala biliyan 26, an ba da rahoton cewa tana da tushe mai ƙarfi na masana’antu.

An ce gwamnatinta na bada tallafi ga ƙanana da matsakaitan masana’antu tare da buɗe wuraren sarrafa kayayyakin da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje. Saboda ƙarancin yawan jama’arta, tana da babban arziki na kowane mutum Dala 10,448.

“Ƙasar kuma tana da masu samar da kayan ƙera motoci ga manyan kamfanonin motocin irin su BMW, Audi, da Opel. Har ila yau, tana da masana’antun yanke lu’u-lu’u,” inji rahoton.

Ghana mai arzikin GDP na Dalar Amurka biliyan 226, an ce tana da ɓangaren masana’antu da suka bunƙasa inda manyan kayayyakin da ta ke fitarwa su ne zinari, wake da kuma ɗanyen mai. Rahotanni sun ce Ghana na qera wayoyinta da na’urorin lantarki da ma motocin lantarki.

Abin takaici ne yadda Nijeriya, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Uwar Afirika’, ba ta cikin wannan jerin. Kusan dukkan ƙasashen da ke cikin jerin ba su kama ƙafa da Nijeriya ba wajen yawan albarkatun ƙasa da na ɗan Adam. Abin da muka rasa shi ne yadda za mu yi amfani da albarkatunmu mu mayar da su hanyar samun arziki.

A cikin shekarun da suka wuce, mun kasance ƙasa mafi cin abinci maimakon samar da shi. Noma ya tava zama jigon tattalin arzikinmu. Akwai dala na gyada a Arewa, koko a Kudu maso Yamma da dabino a Kudu maso Gabas.

Kowanne daga cikin yankuna ya shiga cikin hanyoyin da tattalin arzikin ya bunƙasa. A lokacin ne Malesiya ta ari dabino daga Nijeriya. A yau ƙasar Malesiya tana gaban Nijeriya wajen noman dabino.

Zuwan ɗanyen mai ya ƙara dagula mana halin da muke ciki. Yawancin mutane sun yi watsi da noma sun shiga harkar mai. Kuɗi sun shiga cikin asusunmu amma ba mu san me za mu yi da su ba. Mun tsunduma cikin harkar shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje kuma ba mu damu da yin sana’o’i masu inganci da za su samu ƙarin kuɗaɗen shiga ba.

Hatta kuɗaɗen da ake samu daga man fetur, wanda shi ne babban abin da muke fitarwa zuwa ƙasashen waje, ba a ƙididdige shi sosai.

Satar man fetur ta janyo asarar biliyoyin daloli na kuɗaɗen shiga. Yanzu da kasuwancin man fetur ya daina zama kamar yadda yake a da, al’ummar ƙasar na ta faman jigata.

Tushen matsalolinmu a matsayinmu na al’umma shi ne nakasar shugabanci. Tun daga ’yancin kai har zuwa yau, ba mu yi sa’ar samun haziƙan shugabanni ba, masu son kishin qasa ba, waɗanda za su kai al’ummar ƙasar nan zuwa inda ake so. Ga mafiya yawan shugabanninmu, abin da suke bi shi ne kwace dukiyar al’umma don son rai.

A wani lokaci cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a ƙasar. Ko a halin yanzu, duk da alƙawarin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗauka na magance wannan dodo, abin ya ci gaba da ruruwa. An zargi Akanta Janar na Tarayyar Nijeriya da aka dakatar, Ahmed Idris, da karkatar da naira biliyan 109 na kuɗaɗen gwamnati.

Ya zuwa yanzu dai ya mayar da naira biliyan 30 kacal. Ya zuwa yanzu dai Nijeriya na ci gaba da ƙoƙarin kwato abin da aka fi sani da satar Abacha a sassa daban-daban na duniya. Marigayi Janar Sani Abacha ya kasance tsohon shugaban ƙasa wanda ya yi mulki da ƙarfen ƙafa tare da tara dukiyar qasa a asusunsa na ƙetare. Ba shi kaɗai ba ne shugaba mai cin hanci da rashawa, don kawai nasa ya fi fitowa fili ne.

Cin hanci da rashawa da gazawar shugabanci ya haifar da gurgunta tattalin arzikinmu. Ya shafi samar da muhimman ababen more rayuwa, kamar wutar lantarki, tituna da layin dogo waɗanda za su iya sauke nauyin yin kasuwanci a Nijeriya. Sakamakon haka, kamfanoni da yawa sun ƙaura zuwa wani wuri. Wasu da yawa sun naɗe.

Wannan ya ƙara taɓarɓarewar rashin aikin yi, wanda bisa ra’ayin mazan jiya ya kai sama da kashi 33 cikin ɗari. Ya ƙara taɓarɓarewar talauci da yunwa. Har ila yau, rashin tsaro ya tashi zuwa matakin da ba za a iya jurewa ba. Tare da duk waɗannan abubuwa, ba abin mamaki ba ne yadda ƙasar ta gaza shiga jerin ƙasashe 12 mafi ci gaba a Afirka.

Abin da muke buƙata a yanzu shi ne ingantacciyar shugabanci da zai ciyar da ƙasar nan qasa mai albarka da kuma tarbiyya. Wannan shi ne abin da ya taimaki Singapore, Malaysia, Indonesia da sauran manyan ƙasashen na Asiya. Wannan shi ne abin da ke faruwa ga Maroko, Masar, Ghana, Afirka ta Kudu da sauran su.

Wannan shine dalilin da ya sa shekarar 2023 ta zama fata ga Nijeriya. Shekara ce ta babban zaɓenmu. Ya zama wajibi ga ‘yan Nijeriya su yi watsi da duk wani gurɓataccen tunani, su zavi ’yan takarar da suka yi aiki, masu cancanta, marasa son kai, masu kishin ƙasa. Ba za mu iya sake yin ƙasa a gwiwa ba a wannan shekara.