Nijeriya da Sao Tome za su yi haɗin gwiwa wajen yaƙi da matsalar tsaro

Daga AISHA ASAS

Nijeriya ta bayyana cewa za ta yi aiki tare da ƙasar Sao Tome wajen yaƙi da matsalolin tsaron don amfanin ƙasashen biyu

Babban Hafsan hafsoshin rundunar tsaro na Nijeriya, Janaral Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a lokacin ya karɓi banƙuncin takwaransa na ƙasar Sao Tome, Janar Idalecio Pachire, a ofishinsa da ke Abuja.

Irabor ya ce had’ɗin kai tsakanin mayaƙan ƙasashen biyu na da matuƙar amfani, musamman wajen tunkarar matsalar tsaro da ake fama da ita a wannan zamani.

Tattaunawar jagororin biyu ta taɓo batun ƙalubalen tsaro a gabar tekun Guinea da irin rawar da ƙasashen biyu ke takawa.

Irabor ya sha alwashin ci gaba da tunkarar matsalar fashin teku da sauran nau’o’in ɓarnar da ake aikatawa cikin ruwan gaɓar tekun Guinea

Sauran hanyoyin da kuma sojojin ƙasashen biyu za su maida hankali su ne wajen Horas da dakarun ƙasar Sao Tome, Atisayen haɗin gwiwa da sojojin Nijeriya da sauran nau’o’in tallafi ga rundunar sojin Sao Tome.

Yayin ziyarar tasa, Janar Pachire ya ziyarci hedikwatar sojojin ruwan Nijeriya da hukumar tattara bayanan sirri ta rundunar tsaron ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *