Nijeriya na ƙara kwarjini a idon duniya ƙarƙashin Tinubu – Ministan Labarai

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Ministan Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewa, Nijeriya na qara kwarjini samun tagomashi da kwarjini a idon duniya ƙarƙashin kyakkyawan jagorancin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake bai wa ƙasar.

Ministan Labaran ya bayyana hakan ne jiya a tattaunawar da ya yi da Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA) a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ake gudanarwa a New York dake Amurka, inda ya ƙara da cewa, Shugaban Nijeriyar ya ƙara fito da martabar ba wai kawai Nijeriya ita kaɗai ba, a’a, har ma da Nahiyar Afrika bakiɗaya.

“Ziyara ce mai matuƙar ban sha’awa da Shugaban Ƙasar ya gudanar. Ya zo ne ba don Nijeriya kaɗai ba, amma har ma da Afrika,” inji shi.

“Tabbas kun gan shi (Shugaba Tinubu) tare da Shugaban Ƙasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramophosa; kun gan shi da Shugaban Tarayyar Comoros, Shugaba Azali Assoumani, kun gan shi tare da Aaki Hussein na Jordan da Shugaban Ƙasar Angola, inda dukkanninsu suka kasance a shirye suke wajen ganin Nijeriya ta daidaita a inda ta dace da matsayinta.

“daga dukkan alamu duniya tana sake maraba da Nijeriya izuwa ga martabar da ta dace da ita. Abubuwa da dama suna ta faruwa.

“Ana sa ido kan Nijeriya don ganin ta yi jagoranci tafiyar, kuma Shugaba Tinubu yana jan ragamar a halin yanzu. Don haka a yanzu Nijeriya tana sake zama muhimmiyar ƙasa a duniya ta hanyar komawa kan matsayinta da aka san ta da shi.”

Daga nan sai Ministan ya bayar da misali da irin yadda Shugaba Tinubu ya gabatar da tsararre kuma kyakkyawan jawabinsa a gaban Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniyar, inda ya tabbatar da tsarin siyasar dimukraɗiyya a matsayin tsari mafi inganci dake bayar da cikakken ’yanci da jin daɗi da walwala ga al’umma da kuma yadda Afrika ke fama da tashe-tashen hankulan masu tsattsauran ra’ayi a nahiyar ta yadda ta janyo hankalin ƙasashen duniya, don su kawo agaji a yankin.

Daga nan sai Malagi ya yi wa ’yan Nijeriya albishir kan yadda Tinubu ya samu amincewar Kamfanin ExxonMobil, wanda ya yi alƙawarin samar da makamashi 40,000 a matsayin sabon zuba jari a ƙasar.