Nijeriya na ƙara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, cewar Lai Muhammed 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce kowace rana Nijeriya na ƙara samun aminci da zaman lafiya ta kowane ɓangare.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammed, ne ya faɗi haka a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, inda ya bayyana cewa jami’an tsaron Nijeriya sun nuna jajircewa, sun cancanci yabo wajen shawo kan matsalar rikice-rikice da matsalar garkuwa da mutane a Arewacin ƙasar.

“Ina alfahari da jami’an tsaron mu maza da mata da ke cin ɗamara, duk da taɓarɓarewar tsaro, ba su karaya ba kuma sun jajirce.

“A daidai lokacin da suka tarwatsa ‘yan ta’adda, sansanonin su, wasu dubbanni tare da iyalansu na miƙa wuya tare da aje makamai,” inji Lai.

Ya kara da cewa, “hukumomin tsaro sun tsaya da digadigan su ne bisa jagorancin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke samar musu da kuma sadaukarwar jami’an tsaro da shugabannin su.”

Yadda Gwamnatin Tarayya ta samar da kayan aiki, Muhammed ya bayyana cewa sama da sojoji 1,500 aka ɗauka aiki a rundunar sojin ruwa cikin shekarar nan, yayin da sojojin sama (NAF) suka karɓi sabbin jiragen yaƙin Super Tucano 12 da JF-17 Thunder Fighter guda uku. 

Ya ce dakarun sojin sun yi amfani da jiragen wajen luguden wuta ta sama da aimaka wa sojin ƙasa, da kuma lalata sansanonin ‘yan bindiga da makamansu.