Nijeriya na buƙatar ƙarin madatsun ruwa domin shawo kan ambaliya – Ali Dala

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Daraktan Kula da Ayyukan Madatsun Ruwa da Tafki a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya Ali Dala, ya yi kira da a ƙara gina madatsun ruwa domin daƙile illar ambaliya.

Dala ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya jagoranci tawagar kwamitin kula da ingancin madatsun ruwa na ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya zuwa madatsar ruwan Oyan a Abeokuta ranar Asabar.

Dala ya ce, ya kai ziyara madatsun ruwa daban-daban a faɗin ƙasar ne domin ganin yanayin da suke ciki da kuma tantance matsayinsu domin shawo kan ambaliyar ruwa.

Yayin da yake lura da cewa yawancin madatsun ruwa a Nijeriya sun tsufa kuma suna buƙatar gyara tare da inganta su, Dala ya jaddada buƙatar ƙara saka hannun jari a aikin gina madatsun ruwa da kuma kula da su.

Ya kuma yi kira da a riƙa kwasar koguna akai-akai domin kawar da tarkace da kuma inganta ƙarfinsu na sarrafa ruwan da ya wuce kima.

“Na sha faɗa, har ma Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli ya sha ambaton hakan, cewa domin mu shawo kan ambaliyar ruwa yadda ya kamata a Nijeriya, muna buƙatar ƙarin madatsun ruwa.

“A halin yanzu Nijeriya ba ta da adadin madatsun ruwa da ake buƙata domin shawo kan ambaliyar ruwa yadda ya kamata.

“Tarkacen da ke taruwa a cikin tafkunan ruwa na iya rage ƙarfin ajiyar su, tare da hana su iya shawo kan ambaliyar ruwa.

“Ta hanyar ƙara yawan madatsun ruwa da inganta su, za mu iya rage tasirin ambaliya a Nijeriya sosai.

“ƙasa kamar Amurka a halin yanzu tana da madatsun ruwa 92,000, Chana na da madatsun ruwa kusan 98,000 yayin da a Nijeriya muna da madatsun ruwa 408 kacal.

“Saboda haka, na yi imanin cewa a lokacin da za mu inganta yawan madatsun ruwa a ƙasar nan, ambaliya za ta zama tarihi ko kuma za ta ragu sosai,” inji shi.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, ana sa ran tantancewar da tawagar za ta yi zai samar da bayanai masu ma’ana kan halin da madatsun ruwa ke ciki a halin yanzu da kuma taimakawa wajen sanar da manufofin da za a ɗauka nan gaba da suka shafi shawo kan ambaliyar ruwa da sarrafa albarkatun ruwa.