Nijeriya na fuskantar tsadar abinci mafi muni cikin shekaru 17 – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A halin yanzu, Nijeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 17 yayin da farashin kayayyaki da ayyuka ya qaru da kashi 20.52 cikin ɗari a cikin watan Agustan 2022 daga kashi 19.64 cikin ɗari da aka samu a watan da ya gabata.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin rahoton ƙididdigar farashin kayan masarufi (CPI) na watan Agusta 2022, wanda aka fitar a ranar Alhamis, 15 ga Satumba, 2022.

A cewar NBS, adadin ya kai kashi 3.52 sama da kashi 17.01 da aka rubuta a watan Agustan 2021.

Rahoton ya kuma nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a birane ya kai kashi 20.95, kashi 3.36 sama da kashi 17.59 da aka samu a watan Agustan 2021.

Yawan hauhawar farashin kayayyaki a yankunan karkara a watan Agustan 2022 ya kai kashi 20.12 bisa ɗari a duk shekara; 3.69 bisa ɗari sama da kashi 16.43 da aka rubuta a watan Agusta 2021.

Dangane da rahoton, an ƙididdige hakan a cikin duk ayyuka na amfanin mutune bisa ga manufar (COICOP) waɗanda suka ba da jigon kanun labarai.

“A duk wata, hauhawar farashin kaya a kanun labarai a watan Agustan 2022 ya kai kashi 1.77, wannan ya kai kashi 0.05 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan Yulin 2022 (kashi 1.82).

Wannan yana nufin cewa a cikin Agusta 2022 farashin kanun labarai (wata-wata) ya ragu da kashi 0.05 cikin ɗari,” inji rahoton.

Canjin kashi a matsakaicin CPI na tsawon watanni goma sha biyu da ya ƙare Agusta 2022 akan matsakaicin CPI na watanni goma sha biyun da suka gabata ya kasance kashi 17.07 cikin ɗari, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 0.47 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 16.60 da aka samu a watan Agustan 2021.

Rahoton ya qara da cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya karu zuwa kashi 23.12 a watan Agustan shekarar 2022 a duk shekara, wanda ya nuna ƙaruwar kashi 2.82 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 20.30 a watan Agustan 2021.

Rahoton ya ƙara yin nazari kan farashin kaya a jihohin Anambra da Ondo sun kasance mafi girma.

“A cikin watan Agustan 2022, hauhawar farashin abinci a kowace shekara ya kasance mafi muni a Kwara (kashi 30.80), Ebonyi (kashi 28.06) da Rivers (kashi 27.64), sai Jigawa (kashi 17.77), Zamfara (18.79%) da Oyo. (kashi 19.80 cikin ɗari) sun sami raguwar hauhawar farashin kayan abinci na shekara-shekara.

“A duk wata-wata, duk da haka, hauhawar farashin abinci a watan Agustan 2022 ya kasance mafi muni a Anambra (kashi 3.05), Ondo (kashi 2.92) da Bauchi (kashi 2.78), yayin da Yobe (kashi 0.46), Oyo (0.89%) da kuma Delta (kashi 0.94) ya sami raguwar hauhawar farashin kayayyaki a wata-wata”.