Nijeriya na neman diyya kan gurɓataccen abincin da aka ba alhazanta a Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta ce, za ta nemi hukumomin ƙasar Saudiyya su dawo mata da kuɗin abincin alhazanta saboda ta ba su gurɓataccen abincin.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, ta ce, Shugabanta na ƙasa, Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana haka a Muna da ke Saudiyya, lokacin da ya ziyarci tantunan alhazai na jihohi.

Ya ƙara da cewa, tuni suka rubuta wasiƙa zuwa ga hukumomin Saudiyya da suka kamata kan yanayin abincin da aka ba alhazan wanda suka yi ta ƙorafi a kan ingancinsa.

Rashin abinci mai kyau dai na ɗaya daga cikin tarin matsalolin da suka yi wa alhazan Nijeriya qatutu yayin aiki Hajjin na bana.

A cewar Zikrullah, an sami matsalar abincin a Muna ne saboda hukumomin Saudiyya ne suka karɓe ragamar ciyar da alhazan, saɓanin yadda ake yi a baya.

Shugaban ya kuma yaba wa alhazan kan haƙuri da fahimtar da suka nuna duk da tarin ƙalubalen, yana mai cewa Aikin Hajji dama ya gaji jarabawa iri-iri.

Daga nan sai ya hore su da su ci gaba da kasancewa jakadun Nijeriya na gari, a ragowar lokacin da ya rage musu a can.