Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya ta bayyana shirinta na cefanar da matatun manta waɗanda take kan gyara su.
Mataimakin na musamman ga shugaban ƙasa kan sadarwa da yaɗa labarai, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan ta shafinsa na ɗ a ranar Lahadi bayan bayyana irin nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a ɓangaren man fetur.
“Ana shirin cefanar da matatun man fetur ɗin Nijeriya da ke Fatakwal da Warri da Kaduna domin bai wa ‘yan kasuwa damar shiga a dama da su wajen samar da wadataccen mai kamar matatar man ɗangote da kawo ƙarshen dogon layin da akan samu a gidajen mai.”
Nijeriya na da matatun mai guda 4 inda biyu ke jihar Fatakwal da Ribas waɗanda suka haɗu suka samar da kamfanin matatar man Fatakwal da ake da ƙarfin tace mai ganga 210,000 a rana. Sai kamfanin matatar man Kaduna (KRPC) wacce ke da ƙarfin tace gangar mai 110,000 da kuma kamfanin matatar mai da Warri (WRPC) mai ƙarfin tace ganga 125,000.
A dunƙule matatun gabaɗaya na da ƙarfin tace ganga 445,000 a rana.
Duk da maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wajen kula da matatun man fetur ɗin na tsawon shekaru, matatun sun gaza taɓuka abin a-zo-a-gani.
A watan Mayun 2023, kwamitin majalisar wakilai na wucin-gadi ya ce gwamnatin tarayya ta kashe sama da Naira tiriliyan 11 wajen gyaran matatun daga 2010 zuwa 2023.
Durƙushewar matatun ta sa Nijeriya ta dogara kacokan wajen shigo da mai daga ƙetare wanda ya haifar da hauhawar kuɗaɗen ajiyar Nijeriya na ƙasashen ƙetare.
Gwamnatoci dama sun zo kuma sun yi alƙawarin gyara matatun man domin magance shigo da mai cikin ƙasar nan amma a ƙarshe sai su gaza yin nasara.
A watan Agustan 2023, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar da cewa matatun man za su dawo aiki daga ƙarshen shekarar Disamba amma shiru babu alamun hakan har shekarar ta ƙare.
Haka ma matatar da ake Warri, gwamantin ta ce za ta fara aiki a watanni uku na farkon shekarar 2024, da kuma matatar Kaduna wacce ita kuma aka ware mata zuwa ƙarshen shekarar 2024, sai dai dukkansu ga shi lokacin ya wace kuma babu wani abin nunawa.
Manhaja ta rawaito muku a watan Oktoba cewa, gwamnatin Nijeriya ta gaza cika alƙawuran da ta ɗauka na farfaɗo da matatun man fetur ɗin Nijeriya.