Nijeriya na shirin haƙo ɗanyen mai gangan miliyan huɗu kullum zuwa 2030

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin samar da ganga miliyan huɗu a kowace rana na ɗanyen mai, da kuma ƙafa biliyan 10 na iskar gas nan da shekarar 2030.

Olu Verheijen, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin mai ne ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar Juma’a a Abuja.

Sanarwar ta samu sa hannun Morenike Adewunmi, Manajan masu ruwa da tsaki a ofishin mai ba da shawara na musamman.

Verheijen ta ce, za a cimma wannan buri ne ta hanyar yin gyare-gyare a vangaren, abubuwan da ba a tava ganin irinsu ba na samar da mai da iskar gas da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bayyana.

“Tun da shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayun 2023, gwamnati ta fara aiwatar da sabbin gyare-gyare domin inganta vangaren masana’antarta mai da iskar gas.

“Haka kuma an yi gyare-gyaren da nufin rage tsadar kayayyaki da kuma lokacin gudanar da kasuwanci a fannin da ke ci gaba da zama babbar hanyar samun kuɗin waje ga ƙasar.

“Waɗannan gyare-gyaren da suka haɗa da umarnin shugaban ƙasa guda uku da aka fitar a watan Fabrairun 2024, za su samar da dubun dubatan ayyukan yi, inganta kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje, da ƙara samun kuɗaɗen haraji da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya,” inji ta.

Verheijen ta bayyana cewa, ofishinta ne ke gudanar da ayyukan sake fasalin.

Ta ce a wani babban mataki na ci gaba da sauye-sauyen tsarin da ake yi a masana’antar man fetur da iskar gas, shugaba Tinubu ya amince da fitar da wasu sabbin tsare-tsare guda biyu na ƙarfafa kasafin kuɗi.

Abubuwan ƙarfafawa, a cewarta, sun haɗa da rage harajin VAT da ya shafi iskar gas, dizal, motocin lantarki, da kuma kuɗaɗen haraji don sabbin saka hannun jari a bincike da samar da mai da iskar gas mai yawa.