Nijeriya ta ƙulla yarjejeniya da Brazil don bunƙasa noma a ƙananan hukumomi 774

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamantin Tarayya ta hannun ma’ikatar noma da wadata ƙasa da abinci da kamfanin ƙasar Brazil mai suna Fundação Getulio ɓargas (FGɓ) sun ƙulla wata ‘yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) domin tallafa wa kamfanoni masu zaman kansu wajen ba sa gudunmowa ga bunƙasa samar da takin zamani da sayen irin shuka da tattalin arziƙin noma.

Sakataren dindindin na ma’aikatar noma, Temitope Fashedemi, ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin Nijeriya inda shugaban kamfanin FGɓ, Carlos Iɓan Simonsen Leal, ya sanya hannu a shalkwatar kamfanin da ke Rio de Janeiro ta ƙasar Brazil a yayin taron G20 da aka kammala.

Wannan wani babban mataki ne da Nijeriya ta ɗauka domin ƙulla alaƙa da kamfanin FGɓ, wanda ya yi fice a matsayin kamfani mafi girman ilimin fasaha a ɓangaren noma a duniya.

Ana sa ran cewa wannan shiri zai zaƙulo tare da tallafa wa wani kasuwanci na noma guda ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin 774 da muke da su da liminsa na ƙwarewa da tallafin kuɗi da hanyoyin cigaba mai ɗorewa da bunƙasa tattalin arziƙi.

“Wannan haɗin guiwa zai ba wa Brazil damar yin aiki da ma’aikatar noma ta Nijeriya. Tare da FGɓ, muna fatan bunƙasa kasuwancin kamfanoni masu zaman kansu wajen samar wadataccen abinci,” in ji Fashedemi.

A ƙarƙashin wannan yarjejeniya ana sa ran za a samar da taki da kuma bayen irin hanyar fasaha da samar da kuɗi ta hanyar zuba jari da zai kai Dala biliyan 4.3 daga kamfanoni masu zaman kansu.

A yayin taron dai akwai manyan jami’an ma’aikatar noma da wakilai daga fadar gwamnatin tarayya da suka halarci sa hannun.