Nijeriya ta amince Kamfanin jiragen Emirates su koma aiki a ƙasar

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Najeriya ta amince jiragen kamfanin sufurin jirgin sama na Emirates da ke Dubai su koma jigila a ƙasar kowane lokaci daga yanzu. A yayin da kamfanin jirgin Air Peace da ke Nijeriyar shi ma ya ce zai koma safara zuwa Dubai, daga ranar1 ga watan Maris na 2022.

Sanarwar tana ƙunshe ne a wata wasiƙa da Hukumar Kula da Sufurin Jirgin Sama ta Najeriya (NCAA) mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Captain Musa Nuhu ta rubuta wa shugaban hukumar sufurin jirgin sama ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Saif Mohammed Al Suwaid.

A wasiƙar, hukumar ta Najeriya ta ce bayan nazarin da hukumomin da abin ya shafa suka yi a kan dokokin kariya na korona da hukumomin na Dubai suka gindaya, a yanzu Najeriya ta amince.

Sakamakon ɓullar ƙwayar cutar Korona nau’in Omicron a ƙarshen shekarar da ta gabata, hukumomin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan sun taƙaita sufurin fasinjoji zuwa ƙasar daga Najeriya da wasu ƙasashen Afirka 11, dokar da ta ɗage ranar 29 ga watan Janairun shekaran nan.

Tun da farko Nijeriya da kasar ta Larabawa sun sasanta sabanin da aka samu a tsakaninsu kan gwajin cutar korona da kuma daga bisani sabani kan yawan jiragen da za su riƙa sufuri a tsakanin ƙasashen biyu.

Jirgin na Dubai yana zuwa Najeriya sau 21 a mako, yayin da Air Peace na Najeriya ke zuwa can sau bakwai a sati.