Nijeriya ta dawo da aƙalla mutane 390 da suka maƙale a ƙasar Nijar

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Tarayya ta dawo da ‘yan Najeriya 390 da suka maƙale a Jamhuriyar Nijar, a ranar Talata, ta hannun hukumar kula da ‘yan gudun hijira, masu Ƙaura, da Waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa (NCFRMI), tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi.

An gudanar da aikin ne a makarantar horas da jami’an shige da fice (ITSK) da ke Jihar Kano, inda aka karɓi waɗanda aka dawo da su. Sun haɗa da maza manya 387, mata 2, da jariri guda. Bayan isowarsu, jami’an NCFRMI da na hukumar shige da fice (NIS) sun yi musu rijista da tantancewa domin tabbatar da samun takardu da damar shiga shirye-shiryen tallafi na gwamnatin tarayya.

A jawabin da aka yi a wajen taron karɓar su, jami’in NCFRMI a Kano, Lubah Liman, wanda ya wakilci kwamishinan hukumar, Tijjani Aliyu Ahmed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na da niyyar tabbatar da cewa waɗanda aka dawo da su sun sami cikakkiyar kulawa da haɗewa cikin al’umma. Ya bayyana cewa ana shirin basu horo da tallafi ta shirye-shiryen bunƙasa rayuwa na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ƙarƙashin tsari mai taken sabunta fata.

Har ila yau, Liman ya jinjina wa haɗin kan hukumomin da suka haɗa kai wajen tabbatar da nasarar aikin dawo da waɗannan mutane. Hukumomin da suka halarci taron sun haɗa da NIS, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM), hukumar hana safarar mutane (NAPTIP), hukumar ba da agajin gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ‘Yan sanda, DSS, NSCDC, da Ƙungiyar agajin gaggawa ta Red Cross. Wannan haɗin gwiwa, a cewar Liman, yana da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin da suka shafi ƙaura da tsaron al’umma.