Nijeriya ta fara nesanta kanta daga amsar rancen Ƙasar Chana – Amechi

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahotanni sun bayyana cewa, Nijeriya ta kewaye Ƙasar Chana, inda ta ƙi amsar rancen Dalar Amurka Bilyan 14.4 da ta ke nema, domin gina layin dogo ko digar jirgin ƙasa a kudancin ƙasar. 

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, tuni shirye-shirye sun yi nisa daga ɓangaren Nijeriya don neman rancen kuɗin daga bankin Standard Chartered, wanda ɗan asalin Landan ne. 

Amma wasu masu rahotannin suna ganin cewa, rashin amsar bashin Chana da Nijeriya ta yi kamar Nijeriya tana neman ‘yanta kanta ne daga ɗaurin zargagungun ɗin da ƙasar Chana take shirin yi mata sakamakon ɗimbin bashin da ƙasar take bin Nijeriya. 

A hanzu haka Nijeriya tana ɗauke da dakon bashin ƙasar Chana har na Dalar Amurka biliyan uku da miliyan huɗu.

A yanzu dai haka Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da karɓar bashi daga ƙasar Chana, inda ta dogara ne kacokan ga Bankin Standard Chartered domin samun rancen gina turakun jirgin ƙasa ko layukan dogo guda biyu masu matuƙar muhimmanci ga yankin Kudancin ƙasar. 

A yayin tattaunawarsa da manema labarai ranar Asabar ɗin da ta gabata a Abuja, Ministan Sufuri na Nijeriya, Rotimi Amechi ya bayyana cewa, a yanzu haka Nijeriya da Bankin Standard Chartered suna tsaka da tattaunawa a game da bashin da za su ba su. Kuma a cewarsa Nijeriya tana neman rancen Dalar Amurka Biliyan 14.4 domin yin aikin turakun jirgin ƙasan a kudancin ƙasar. Da niyya ƙara inganta harkar kasuwanci da sufuri takanin gabas da kudancin ƙasar. 

Shi dai Bankin na Standard Chartered da ma banki ne na asalin ƙasar Ingila da  ya saba ba da tallafi na rancen kuɗi ga ƙasashen Afirka da na Asiya. 

Ministan ya ƙara da cewa, duk da dai Nijeriya tana ƙoƙarin nisanta kanta daga abinda ya shafi ƙasar Chana amma tuni Nijeriya sun gama ƙulla yarjejeniya da Kamfanin ƙasar Chana (CCECC) a kan su za su yi aikin gadojin jirgin ƙasan.

A cewarsa, “Nijeriya ta nesanta daga Chana a ayyuka da dama. Kuma yanzu haka ma Ministar Kuɗi, Hajiya Zainab Ahmad ita ce za ta jagoranci tattaunawar tsakanin Nijeriya da Bankin,” inji shi.