Nijeriya ta fi kowace ƙasa matsalar wutar lantarki a duniya – Adesina

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwunmi Adesina, ya bayyana cewa NIjeriya ce ta fi kowacce ƙasa yawan al’ummar da ke fama da rashin wutar lantarki a duniya.

Adeshina ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekaru 90 na tsohon shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon.

Ya bayyana cewa kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 86 ne ba su da wutar lantarki, lamarin da ya sanya ƙasar ta zama kan gaba a duniya a wannan fanni.

Adeshina ya kuma ƙara jaddada cewa rashin ingantaccen wutar lantarki na gurgunta harkokin kasuwanci da masana’antu a faɗin ƙasar nan.

“Hukumar IMF ta yi kiyasin cewa Nijeriya na asarar kusan dala biliyan 29 a duk shekara ko kuma kashi 5.6 saboda rashin ingantaccen wutar lantarki. Rahoton ya kuma nuna cewa Nijeriya na kashe dala biliyan 14 a duk shekara wajen samar da mai ga janareta.

Rashin wutar lantarki yana kashe masana’antun Nujeriya. A yau, babu wata sana’a da za ta cigaba da wanzuwa a Nijeriya ba tare da janareta ba.

“Nujeriya na da iskar gas da ɗanyen mai da yawa, amma duk da haka mutane miliyan 86 na rayuwa a kullum ba tare da wutar lantarki ba. A yau Nijeriya ce ƙasa ta ɗaya a duniya wajen yawan mutanen da ba su da wutar lantarki,” inji Adesina.