Daga USMAN KAROFI
Hukumar kula da shaidar ɗan Ƙasa ta Nijeriya (NIMC) ta gano sama da ‘yan Nijar 6,000 da aka yi wa rijistar lambar shaidar ɗan kasa (NIN) ba bisa ƙa’ida ba. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin kafa kwamitin ministoci don tabbatar da cikakken bayani kan rajistar jin ƙai da gwamnatin tarayya ke amfani da ita wajen shirye-shiryen tallafi.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ke da alhakin kula da NIMC, ya bayyana hakan yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Talata, 4 ga Fabrairu, 2025. Ministan ya ce lambar NIN din da ba bisa ƙa’ida aka samu an cire su daga bayanan hukumar yayin wani aikin tsaftace rajista.
A baya dai, a ranar 13 ga Oktoba, 2022, rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yin rijistar NIN na bogi ga ‘yan ƙasashen waje a sansanin ‘yan gudun hijira na Gagamari da ke Jamhuriyar Nijar. An same su da na’urorin rijistar NIN, injin buga takardu, kwamfuta da wasu kayayyakin aiki da ke nuna cewa suna gudanar da aikin ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar wata majiya daga fadar shugaban ƙasa, Shugaba Tinubu yana son ganin an inganta rajistar jin ƙai ta ƙasa, domin tabbatar da cewa tallafin gwamnati yana zuwa ga waɗanda suka cancanta. An kuma ce NIMC na ƙoƙarin tabbatar da cewa waɗanda ke cikin rajistar suna da ingantacciyar shaida ta NIN domin gujewa bayar da tallafi ga sunayen bogi.
Shugabar NIMC, Coker-Odusote, ta bayyana cewa tsaftace bayanan zai tabbatar da inganci da gaskiya wajen biyan kuɗaɗen tallafi ga mutanen da suka cancanta. Ta kuma ce matsalar da aka samu a rijistar NIN-SIM ba daga NIMC ta fito ba, illa kawai matsala ce daga ɓangaren kamfanonin sadarwa, wanda yanzu an magance ta.