Nijeriya ta karɓi rigakafin korona na farko, Buhari da mataimakinsa za su tsayar da ranar da za a yi musu rigakafin

Shugaba Buhari

Daga AISHA ASAS

A balin da ake ciki, maganin rigakafin xutar korona na AstraZeneca ya iso Nijeriya.

Wannan shi ne rigakafin korona na farko da Nijeriya ta samu wanda ake sa ran za a yi wa ‘yan ƙasa bayan gwamnati ta kammala tsare-tsarenta gane da rigakafin.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, za su tsayar da ranar da kowannesu zai yi allurar rigakafin cutar korona a idon duniya ta hanyar amfani da rigakafin Oxford/AstraZeneca na rukunin farko guda milyan 4 da Nijeriya ta karɓa a wannan Talata.

Darakta a Hukumar Bunƙasa Kula da Lafiya na Matakin Farko na Ƙasa (NPHCDA), Dr. Faisal Shuaib ne ya sanar da hakan yayin da Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Yaƙi da Cutar Korona ke gabatar da bayanin ayyukansa a Abuja kamar yadda ya saba.

Shuaib ya ce, Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin PTF kan yaƙi da cutar korona, Boss Mustapha, zai haɗa kai da waɗanda suka dace wajen tsayar da ranar da za a soma yi wa ‘yan ƙasa rigakafin korona da nufin kare ‘yan ƙasa daga barin kamuwa da ita.

Ta bakin Shuaib, “Ina mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa an yi dukkkan abin da ya kamata domin karɓa da ajiya da kuma samun nasarar yi wa ‘yan ƙasa rigafin korona.

“Akwai ƙwarya-ƙwaryan bikin da za a gudanar ƙarƙashin shugabancin shugaban kwamitin PTF a sashen masaukin manyan baƙi na babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, yayin karɓar rigakafin ban ya iso.

“A ƙarshen bikin, za a ɗebi maganin a miƙa wa hukumar NAFDAC don ta yi nazari a kai na tsawon kwana biyu (wato daga Laraba, 3 ga wata zuwa Alhamis 4 ga Maris).

“Bayan duka hukumomin da suka dace da shugabanni sun gamsu, za a tafi da maganin Babbar Asibitin Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 5 ga Maris, 2021, inda za a shirya wurin farko na yin rigakafin inda za a soma da jami’an kula da lafiya da ke kan gaba wajen yaƙi da annobar korona…..”

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*