Nijeriya ta kasa ɗaukar mataki watanni shida bayan rahoton zanga-zangar ENDSARS – HRW

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch ta zargi hukumomin Nijeriya da ƙin ɗaukar matakin tabbatar da adalci ga masu zanga-zangar neman kawo ƙarshen zaluncin ‘yan sanda wato #ENDSARS, a Jihar Legas a 2020, bayan wata shida da kwamitin binciken da aka kafa ya zargi jami’an tsaro da cin zarafin mutane a lokacin.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin, ta buƙaci gwamnati da ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar a ɗauka a kan waɗanda aka zarga da aikata laifi.

Ƙungiyar ta ce, ba zai yiwu a kawar da kai a kan rahoton ba, ba tare da wani abu ya biyo bayan hakan ba a kan waɗanda ake zargi da kisa da kuma jikkata masu zanga-zangar.

Ta ce muddin ba a ɗauki mataki ba a kan shawarwarin kwamitin, hakan zai harzuƙa waɗanda abin ya shafa, tare kuma da ƙarfafa wa jami’an tsaro guiwa kan cin zarafi.

A watan Oktoba na 2020 ɗaruruwan matasa suka kwarara a titunan biranen wasu jihohin Nijeriya, suna zanga-zangar neman a rushe rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaƙi da ‘yan fashi da makami, wato SARS, wadda ta yi ƙaurin suna da cin zarafin jama’a, tare kuma da kawo ƙarshen zaluncin da ‘yan sanda ke yi, abin da ya janyo jami’an tsaro suka mayar da martani da ƙarfin da ya wuce kima.

Ɗaya daga cikin inda lamarin ya fi ƙamari shi ne na mashigar Lekki da ke Legas wato Lekki Toll Gate, inda aka bayar da rahoton cewa sojoji da ‘yan sanda sun buɗe wuta a kan masu zanga-zangar, har suka kasahe tare da jikkata mutane, abin da su kuma suka musanta.