Nijeriya ta naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles

Daga WAKILINMU

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayar da sanarwar naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles a ranar Laraba.

Hukumar ta ce, Jose Peseiro wanda ɗan asalin ƙasar Portugal ne shi zai maye gurbin Gernat Rohr da ta kora.

Tuni NFF ta naɗa Augustine Eguavoen a matsayin kocin riƙon ƙwarya domin ya ja ragamar Super Eagles a yayin da ake shirin soma gasar cin kofin Afirka.

A cikin sanarwar da ta fitar NFF ranar Laraba ta ce kwamitin zartarwata ne ya amince da naɗa Peseiro ne bayan raba gari da Gernot Rohr.

“Kwamitin ya amince Augustine Eguavoen a matsayin kocin riƙon ƙwarya ya jagoranci Super Eagles a gasar cin kofin Afrika Afcon 2021 a Kamaru yayin da kuma Peseiro zai zama mai sa ido.”

Jose Peseiro wanda tsohon kocin ƙungiyar Sporting Lisbon da Porto ne, ya horar da Venezuela da Saudiyya.

Ya horar da ƙungiyoyi a Afirka da ƙasashen Larabawa da suka haɗa da Al ahly ta Masar da Al Hilal ta Saudiyya.

Wane ne Jose Peseiro?
Peseiro ya tava riƙe mukamin mataimakin koci a ƙungiyar Real Madrid a tsakanin shekarun 2003-2004.

Naɗa Peseiro a matsayin sabon kocin tawagar ‘yan wasan na Nijeriya na zuwa ne sama da makonni biyu bayan da aka sallami Gernot Rohr.

Peseiro

Bayan sallamar Rohr hukumar ƙwallon ƙafar ta NFF ta naɗa Augustine Eguavoen a matsayin kocin wucin gadi.

An haifi Peseiro a ranar 4 ga watan Afrilun 1960 a garin Coruche da ke ƙasar Portugal.

A zamanin da yake buga ƙwallonsa, Peseiro ya kasance ɗan wasan gaba a tawagar ‘yan wasan ƙasarsa ta Portugal.

Ya kuma horar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama ciki har da Sporting CP wacce ya kai gasar UEFA a shekarar 2005.

Ɗan shekara 61, Peseiro ya kuma horar da ‘yan wasan Venezuela, Sporting Lisbon, FC Porto da ƙungiyar Al Ahly ta ƙasar Masar.

‘Yan wasan Venezuela, su ne tawagar da ya horar ta ƙarshe kafin NFF ta ɗauke shi aiki.

Haka zalika, Peseiro ya tava zama mataimakin koci a ƙungiyar Real Madrid a tsakanin shekarun 2003-2004.

Wata sanarwar bayan taro da hukumar ta NFF ta fitar ta nuna cewa, Peseiro zai karɓi raganar tafiyar da ‘yan wasan na Super Eagle ne bayan an kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON da za a fara a Kamaru.

A ranar 9 ga watan Janairun shekara mai kamawa za a fara gasar ta AFCON za kuma a kammala a ranar 6 ga watan Fabrairun 2022.

Augustine Eguavoen da aka ba riƙon ƙwarya ne zai kai tawagar ‘yan wasan ta Super Eagle gasar, ko da yake, shi ma Peseiro zai halarci gasar, amma zai je ne a matsayin mai sa ido kamar yadda NFF ta ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *