Nijeriya ta naɗa Salisu Yusuf sabon kociyan Super Eagles

Daga WAKILINMU

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF), ta sanar da naɗa Salisu Yusuf a matakin sabon kociyan Super Eagles ta gida da ke buga gasar CHAN.

Haka kuma zai ja ragamar tawagar matasan ƙasar ta ‘yan ƙasa da ke buga wasannin Olympics.

Yusuf ya taɓa jan ragamar Super Eagles B a gasar kofin Afirka ta ‘yan wasa da ke taka leda a gida a Morocco, inda Nijeriya ta yi ta biyu a 2018.

Kamar yadda NFF ta sanar a shafinta a Intanet ranar Alhamis ta ce zai yi aiki tare da Kennedy Boboye da Fatai Osho da Abubakar Bala Mohammed da kuma Fidelis Ikechukwu a matakin mataimaka.

Shi kuwa Eboboritse Uwejamomere zai yi aiki a matsayin mai tantance yadda wasa ke gudana wato Match Analyst, yayin da aka naɗa Ike Shorounmu da kuma Suleiman Shuaibu a matakin kociyan masu tsaron raga.

Haka kuma NFF ta ce, nan gaba kaɗan za ta sanar da sabon kociyan babbar Super Eagles da zarar ta cimma yarjejeniya da shi, sannan ta gabatar da shi.

Hukumar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta rusa masu horar da Super Eaglees ƙarƙashin jagorancin Augustine Eguavoen, bayan da ya ƙasa kai ƙasar gasar kofin duniya da za a yi a Ƙatar a bana – Ghana ce ta yi nasara a kan Nijeriya da ci 2-1, bayan da suka tashi 0-0 a Ghana.

Sauran naɗe-naɗe da NFF ta yi a ranar Alhamis, Ladan Bosso zai cigaba da aikinsa na jan ragamar U20 ta maza.

Zai yi aiki tare da tsohon kocin matasan Nijeriya U17 Fatai Amao, sai waɗanda za su taimaka masa da suka haɗa da Oladuni Oyekale da Jolomi Atune Alli da kuma Baruwa Olatunji Abideen a matsayin mai horar da masu tsaron raga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *