Nijeriya ta rasa damar karɓar baƙoncin gasar kofin Afrika ta 2027

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Nijeriya ta rasa damar karɓar baƙoncin gasar kofin Afrika, bayan da aka bayyana sunan ƙasashen Kenya da Uganda da kuma Tanzania a matsayin ƙasashe uku da za su yi tarayya wajen karɓar baƙoncin gasar ta 2027.

Gasar ta 2027 za ta zama karon farko da za ta gudana a gabashin Afrika tun bayan shekarar 1976 lokacin da Habasha ta karɓi baƙoncinta.

A ɓangare guda makamanciyar gasar da za ta gudana a shekarar 2025 an mika damar ɗaukar nauyinta ga a Moroko bayan da Algeria da Zambia suka janye.

Tun farko Nijeriya da Benin suka nemi yin haɗin gwiwa wajen ɗaukar nauyin gasar amma suka rasa damar.

A Talatar da ta gabata ne hukumar ƙwallon ƙafar Afrika ta sanar da jerin ƙasashen da suka yi nasarar samun damar ɗaukar nauyin gasar wadda ke gudana duk bayan shekaru 2 yayin taron da ya gudana a Masar.

Rabon da Nijeriya ta samu damar ɗaukar nauyin gasar dai tun a shekarar 1980 lokacin da Christian Chukwu ya jagoranci tawagar ƙasar ga nasara gaban dubban magoya baya ciki har da shugaban ƙasar na waccan lokaci Shehu Shagari.

Haɗin gwiwar ɗaukar nauyin gasar da Nijeriya ta yi tsakaninta da Ghana a shekarar 2000 ya zo da rashin nasara bayan da Kamaru ta lashe kofin yayin wasan karshe da ya gudana a Legas.

“Ina matuqar alfahari da Maroko,” in ji shugaban CAF Patrice Motsepe bayan bayyana sunayen masu karvar baƙoncin gasar a Alkahira.

“Ƙasashen da suka fafata a Moroko (na gasar 2025) – Algeria, Zambia da Nijeriya-Benin – sun sanar da janyewarsu, koda kuwa har yanzu waɗannan ƙasashen sun gabatar da nasu jawabin,” in ji shi.

“Babban dalili shi ne ta goyi bayan Maroko a takararta a gasar cin kofin duniya ta 2030,” in ji Motsepe tare da Spain da Portugal.

Morocco tana alfahari da filayen wasa da yawa na duniya kuma ta yi nasarar karɓar baƙoncin gasar ƙwallon ƙafa ta Afirka da na duniya da dama.

Sai dai Kenya da Tanzaniya suna da filin wasa guda daya ne kacal kowannensu da Uganda ba ko daya, wanda hakan ya tilastawa ‘yan wasan ƙasar buga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2023 a wuraren da babu ruwansu.

“Daya daga cikin mahimman manufofin shi ne shawarar da aka yanke a yau (yana inganta) ci gaban ababen more rayuwa da filayen wasanni (da kuma) ya zama tushen farin ciki a tsakanin matasa,” in ji Motsepe.