Nijeriya ta sake ƙwato kambunta na ƙasar da ta fi zarra a samar da man fetur a Afirka

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai ƙasar Nijeriya ta sake yi wa ƙasar Angola fintinkau a matsayin ƙasa mai samar da mafi yawan man fetur a Afirka.

Wato kenan ta sake ƙwato kambunta wanda aka santa da shi a baya a matsayin ƙasar da ta fi kowacce samar da man fetur a Afirka.

Wannna bayani yana ƙunshe ne a wani jawabi da ƙungiyar ƙasashe masu samar da man fetur (OPEC) rmta saki game da samar da ɗanyen man fetur a cikin watan Mayun 2023.

Amma a watan Afrilu ƙasar Angola ta kere Nijeriya wajen samar da man fetur ɗin.

A halin yanzu dai Nijeriya ta ɗare matsayi na farko a gurbin jerin manyan ƙasashen da suke samar da man fetur a Afirka.

Wato ta zarce su Libya da Angola bayan ta samar da gangar man har miliyan 1.18 a kowacce rana a cikin watan na Mayu.

OPEC ta bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata a cikin rahotonta a game da man wanda ta saba duk wata-wata na watan Yunin bana.

Rahotanni sun bayyana cewa, adadin man da Nijeriya take samarwa ya ƙaru da ganguna 185,000 wato daga ganga 999,000 da ake samarwa a kowacce rana a watan Afrilu, zuwa ganga miliyan 1.18 a yanzu.

Ƙasar Libya ita kuma ta samu koma-baya a nata ɓangaren bayan man da take samarwa a kullum ya ragu da ganga 52,000. Sai dai ya ɗaga zuwa ganga miliyan 1.15 kowacce rana saɓanin ganga miliyan 1.21. Abinda ya ba ta damar samun matsayi na 2.

Ƙasar Angola kuma ta samu matsayi na uku da ganga miliyan 1.11 a kullum.

Hakazalika, OPEC ta bayyana jimillar man fetur ɗin da ake samarwa a duniya ya ƙaru zuwa ganga miliyan 28.06 kowacce rana a watan Mayun 2023.

Rahotanni kuma sun bayyana cewa, hakan ba ya rasa nasaba da ƙaruwar man da ake iya samarwa a Nijeriya Iran da kuma Angola.