Nijeriya ta samu ƙarin mutum 240 da suka harbu da cutar korona

Daga WAKILINMU

An bada sanarwar cewa Nijetiya ta samu ƙarin wasu mutum 240 da suka kamu da cutar korona a ‘yan sa’o’in da suka gabata.

Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ce ta bada sanarwar haka da daddare a Lahadin da ta gabata, ta shafinta na twita.

Ƙarin da NCDC ta ce an samu ya shafi wasu jihohi ne su 13 kamar haka: Anambra 85, Lagos 82, Osun 17, Ogun 10, Kwara 9, FCT 8, Kano 7, Abia 6, Ekiti5, Borno 4, Edo 2, Bayelsa 2, Kaduna 2 da kuma Rivers 1.

Cibiyar ta ce katafariyar cibiyar bada agajin gaggawa game cutar korona da Gwamnatin Tarayya ta samar (EOC), tana ci gaba da ƙokarin sauke nauyin da aka ɗora mata na yaƙi da wannan cuta.

A cewar NCDC kawo yanzu, adadin waɗanda aka tabbatar da sun kamu da cutar a faɗin Nijeriya ya kai 155,657, mutum 133,768 sun warke, yayin da mutum 1,907 sun rasu sakamakon cutar.