Nijeriya ta samu ƙarin mutum 753 da suka harbu da cutar korona – NCDC

Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta bayyana ceqa an samu ƙarin mutum 753 da suka harbu da cutar korona a faɗin ƙasa a tsakanin sa’o’i ashirin da huɗu da suka gabata.

Cibiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet a safiyar Juma’a, inda ta nuna ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi goma sha huɗu ne.

NCDC ta ce jihohin da lamarin ya sha sun haɗa da: Legas 364, Akwa Ibom 141, Oyo 74, Rivers 46, Abia 38, Ogun 24, Kwara 20, sai kuma Birnin Tarayya, Abuja mai mutum 12.

Sauran jihohin su ne, Ekiti 10, Delta 9, Edo 6, Filato 5, Imo 3 da kuma jihar Bayelsa da take da mutum 1.

Kawo yanzu, NCDC ta baki ɗaya adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da xutar a faɗin ƙasa, ya kai mutum 180,661, yayin da mutum 166,560 sun warke an kuma sallame su, sannan cutar ta kashe mutum 2,200.