Nijeriya ta samu Naira miliyan 278 daga sinima a watan Fabrairu

Daga AISHA ASAS

A ranar Talata da ta wuce, Ƙungiyar Masu Haska Finafinai ta Ƙasa, wato Cinema Exhibitors Association of Nigeria, CEAN, ta sanar da cewa, harkar kasuwar finafinai a Ƙasar Nijeriya ta samu ci baya a watan Fabrairun wannan shekara, domin kasuwar finafinai ta tsaya a iya samun Naira miliyan 200 da 78.

Shugaban ƙungiyar Ope Ajayi, ya shedawa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, a cikin wata tattaunawar da suka yi cewa, sun samar wa Nijeriya Naira miliyan 278 a cikin watan Fabrairu, wanda ya yi ƙasa da abinda aka samu a watan Janairu da ya wuce da suka samar da Naira miliyan 819.

Shugaban ƙungiyar ya ɗora alhakin wannan ci baya kan matsalar canjin kuɗi da kuma ƙaracin sababbin takardun kuɗi, haɗi da raunin sabin ɗin bankuna da ƙasa ta ke fuskata a halin yanzu.

Mista Ajayi, ya ƙara da cewa, tun daga farko, sinima ta fuskanci ƙishirwar sababbin finafinai dalilin ƙaratowar zaɓe, sakamakon masu shirya fim da suke ƙi fitar da sababbin finafinai dalilin kacaniyyar siyasa da ke ɗauke wa mutane hankali.

“Wasu ‘yan dalilai ne ke jan ragamar raguwar kasuwar da muka samu. Daga ciki akwai rasa kasuwar satin zaɓe da muka yi gabaɗaya, sai rashin sabis ɗin POS da ya shafi ƙasa bakiɗaya. Sai kuma masu shirya fim da kuma masu rarrabawa da suka gujewa sakin finafinai a lokacin zave, wannan ya janyo ƙishirwar finafinan da za a haska a sinima,” inji Mista Ajayi.

Ope Ajayi ya ce, manyan finafinai da suka haska a watan Fabrairu ƙwaya biyu ne kawai, wato ‘Antman’ da kuma ‘Love in a pandemic’. Sai dai ya bayyana cewa, a wannan wata na Maris zata canza zane, domin adadin finafinan da za su fita sun haɗa da; ‘Creed III’, ‘What love got to do with it’, ‘Shazam fury of the gods’, ‘John Wick iv’, ‘Different strokes’ da kuma ‘Dungeons and Dragons83’.