Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kamfanin Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), ya yi alƙawarin samar da tsarin ajiyar wuta don tabbatar da cewa ’yan Nijeriya na su riƙa zama cikin duhu ba a duk lokacin da babban layin lantarki ya katse.
Manajan Daraktan TCN, Sule Abdulaziz, ne ya bayyana wannan shirin na wata hira a gudan talbiji na Channels.
Ya zargi tsofaffin ababen more rayuwa da suka kai shekaru 50 da faruwar rugujewar wutar lantarki a ƙasar.
Abdulaziz ya ci gaba da cewa, “A yanzu haka muna ɓullo da wani tsari, kuma Bankin Duniya ne ke ɗaukar nauyinsa, kuma aikin zai ɗauki shekaru biyu ana kammala shi, kuma yanzu mun ƙaddamar da kashi 70 na aikin.
“Kusan wata ɗaya da ya wuce, muna Gwagwalada a Abuja tare da Bankin Duniya inda muka yi bikin aikin. An kammala kashi 70 cikin dari. Da zarar mun sami tsarin watsawa, zai rage yawan samun rikice-rikicen tsarin. Muna ƙoƙarin inganta dukkan layukanmu na lantarki,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa gwamnati ba za ta iya samun isassun kuɗaɗen aikin ba, TCN na haɗa gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu don tara kuɗaɗe.
“Yanzu mai girma minista yana aiki da fadar shugaban ƙasa domin samun wannan amincewar. Wannan shi ne abin da muke kira ‘super grid’.
“A lokacin da muke da shi, ko da akwai aibi a layin sadarwa guda ɗaya, za ku iya canzawa zuwa waccan ta yadda za mu samu madadin amma yanzu, irin grid din da muke da shi, da zarar mun samu matsala a layin. ba ku da wani layin da za ku kunna zuwa gare ku,” inji shi.
Shugaban na TCN ya ce dole ne a ci gaba da saka hannun jarin samar da wutar lantarki mai muhimmanci da kayayyaki masu inganci.
Ya ce, ‘yan Nijeriya na ƙara biyan kuɗin wutar lantarki saboda samar da wutar lantarki ba sauƙi ba ne, kuma ‘yan ƙasar da ke Band A a yanzu suna samun wutar lantarki ta sa’o’i 24, lamarin da wasu mazauna yankin suke nema.
Abdulaziz ya ce, duk da ƙarin kuɗin wutar lantarki, wutar lantarki a Nijeriya ya kasance mai rahusa fiye da yadda ake samu a aasashen Chadi, Mali, Burkina Faso, da sauran ƙasashen Afirka.