Nijeriya za ta ƙaddamar da shirin zaman kotu na zamani ‘Virtual’ – Malami

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya bayyana cewa, an shirya tsaf don ƙaddamar da shirin shari’o’in kotun ƙoli na zamani ‘Virtual’ a cibiyoyin gyaran hali na Nijeriya.

Malami ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Dakta Umar Gwandu, mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce, shirin zai fara aiki ne daga cibiyar gyaran hali na Kuje da ke Abuja a ranar 6 ga watan Disamba.

“Waɗanda ake sa ran a wajen taron sun haɗa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, da Kotul-janar na Hukumar Kula da Gidaje Yari ta Nijeriya, Halilu Nababa, da kuma mambobin kwamitin Shugaban ƙasa kan cibiyoyin gyara hali da rage cunkoso,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, ma’aikatar tare da haɗin gwiwar kwamitin shugaban ƙasa kan gyara hali da rage cunkoso, suna hanzarta yin cuɗanya da cibiyoyin gyaran hali na Nijeriya don ba da damar a kai shaidun waɗanda ake tuhuma a gidan yari ba tare zuwa gaban kotu ba, don kaucewa kawo cikas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *